Tashin Hankali Yayin da Mata Ta Kama Kanwar Na Alfasha da Mijinta, Saura Wata 3 Auren Kanwar

Tashin Hankali Yayin da Mata Ta Kama Kanwar Na Alfasha da Mijinta, Saura Wata 3 Auren Kanwar

  • Wata matar aure da ke sana’ar siyar da abinci ta shiga tashin hankali bayan da ta kama kanwarta da kwanciya da mijinta
  • Matar mai shekaru 33 ta kasance da mijinta tsawon shekaru biyar, ta kuma dauki lokaci tana taimakawa kanwar tata a fannin karatu
  • A yanzu, mijin ya shiga firgici da yadda ta yi shiru ta kyale shi duk da abin da ya faru tsakaninsa da kanwar, ta tura kanwar gida

Wata mata tana neman shawari bayan da ta kama mijinta dumu-dumi yana lalata da kanwarta a kan kujera a gidanta.

Wata mata a TikTok da ta yada labarin ta ce wata mata mai shekaru 33 ce ta turo sakon neman shawari, tare da cewa matar na sana’ar siyar da abinci, mijin kuwa dan kasuwa ne.

Matar ta kasance da aure tsawon shekaru biyar, kanwarta kuma saura watanni uku kacal ya rage mata ta yi aure.

Kara karanta wannan

Budurwa ta Kwace Motar da ba Saurayinta bayan Shekatu 2 da Suka Rabu, Kazantar da ta Gani Ciki ta Tada Hankali

Matar aure ta kama mijinta na aikata alfasha da kanwarta uwa daya uba daya
Tashin Hankali Yayin da Mata Ta Kama Kanwar Na Alfasha da Mijinta | Hoto: Frizkes
Asali: Getty Images

Matar ta kuma bayyana cewa, ita ke daukar nauyin kanwar a karatunta na ilimin jinya, saboda mahaifinsu ya rasu, kuma basu da hali ga mahaifiyarsu ba laifiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya faru

Ta ba da labarin yadda lamarin ya faru, inda tace sau tari ba ta zama a gida saboda yanayin sana’arta don haka take da abinci ga kanwar ta ba mijinta.

Wannan kuwa na faruwa ne saboda kanwar na zama da ita duk lokacin da take hutun makaranta.

A irin wannan yanayin ne ta aike kanwar watarana ta kai ma mijinta abinci gida, sai ta biyo don duba wani abu, kawai ta kama su suna alfasha.

Ta ce:

“Ji nayi kamar zan yi hauka...Wannan kanwar tawa an yi baikonta za ta yi aure nan da watanni uku kacal.”

A cewarta, tun faruwar lamarin, mijin a tsorace yake, domin bata kula shi ba, yana kuma tsoron za ta bashi guba ya ci ya mutu.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Gano Mijinta Ya Yi Amarya a Ɓoye Har Sun Haihu, Ta Je Gidan An Buga Dirama a Bidiyo

Ta ce bata san ta yadda za ta fara fada ma mahaifiyarsu da ke dauke da hawan jini ba. Amma dai ta tura kanwar tata gida.

Ga dai bidiyon neman shawarin da matar ta aiko:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

kindness Agu:

“Ki tambaye idan suna son juna, idan haka ne ke kyale su ki yi tafiyarki cikin kwanciyar hankali sannan ku bude zuciyarki ga neman wata soyayyar, amma ki nisanci kanwarkin nan.”

rowdiest:

“Ki yi hakuri❤️, ya kamata mata su mai da hankali ga aurensu. Kada kike bari mijinki ya dawo gida kafin ki dawo, ki daura gidanki a kan turba.”

julietchukwuma857:

“Kai mata:idan kuna da aure don Allah kuke yiwa mazanku hidima musamman abinci saboda akwai danko tsakanin miji da da mata da abinci:ki dauka ko ki bari.”

Emily Edward635:

“Kada ki yi maganar tare da shi. Amma ki yi maganar da mijin kanwarki saboda ta san halin da kika shiga.”

Kara karanta wannan

Bidiyo: Daga Dirarriyar Budurwa Zuwa Sukurkutacciyar Matar Aure, Ta Fashe da Kuka Tare da Dora Laifi kan Mijinta

@Silinbabs0:

“Bai kamata tace masa komai ba kawai ta sanar da saurayin da zai auri kanwar tata saboda ta ji zafin da ta ji iata ma.”

Wata mata kuwa kama mijinta ta yi yana cimar tuwo da miya bayan da suka yi alkawarin yin azumin kwanaki shida a jere, bidiyon ya ba da mamaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.