2023: An Sanar da Ranar Da Za A Fada Wa Kiristocin Kudancin Kaduna Dan Takarar Gwamna Da Za Su Zaba
- Apostle Emmanuel Kure, shugaban kungiyar kiristocin kudancin jihar Kaduna ya ce ranar 14 ga watan Janairun 2023 za su fada wa mambobinsu wanda za su zaba gwamna
- Kure ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da addu'a da kungiyar ta yi a garin Kafanchan da ke Kaduna a ranar Litinin
- Jagoran na kiristoci ya kuma ce dole wanda za su zaba ya zama mutum mai tsoron Allah kuma wanda ya fahimci yadda ake mulki na gida da waje
Kafanchan, Kaduna - Shugabannin kungiyar kiristoci na Kudancin Kaduna sun tsayar da ranar 14 ga watan Janairun 2023, a matsayin ranar da za su fada wa kiristoci wanda za su zaba a zaben gwamnan 2023 na Kaduna.
Kamar yadda The Punch ta rahoto, shugaban kungiyar, Apostle Emmanuel Kure, ne ya bayyana hakan yayin taro tsakanin kungiyar da yan takarar gwamna a jihar, da addu'a da aka yi a Kafanchan a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce abubuwa da za su duba wurin zaben dan takarar, Apostle Kure ya ce tsoron Allah na cikin abin da dole dan takarar da za su zaba ya kasance yana da shi.
Kure ya ce:
"Dole ne dan takara ya kasance yana da kyakkyawar fahimtar shugabanci a cikin gida da kasar waje, don samun ci gaba mai ma’ana a kudancin Kaduna da jihar baki daya.
"Dole dan takarar gwamna ya nuna sha'awar yaki da rashawa wanda ya zama cikas ga cigaban al'umma idan yana son goyon bayan mutane."
Kure ya yi tsokaci kan rikici a kudancin Kaduna
Da ya ke magana kan rikici a jihar musamman kudancin Kaduna, Apostle Kure ya ce abin ya isa kuma ya bukaci a yi sulhu na gaskiya tsakanin mutanen kudanci da arewacin jihar, rahoton The Punch.
Shahararren malamin addini ya fada wa mutane kada su zabi jam'iyyar APC a zaben 2023
A wani rahoton, Rabaran Mathew Ndagoso, babban limamin darikar katolika a Kaduna, ya hori kiristoci kada su sake su zabi jam'iyyar APC mai mulki a babban zaben shekarar 2023 da ke tafe saboda tsayar da yan takarar musulmi biyu.
Rabaran din ya ce tsayar da yan takara mabiya addini daya ya saba ka'idar adalci, daidaito da hadin kai a kasa mai yalwa irin Najeriya, rahoton Channels TV.
Asali: Legit.ng