Sanusi Ya Yabi Sabon Tsarin Rage Cire Kudi, Yace Za Ayi Maganin ‘Yan Siyasa a 2023
- Malam Muhammad Sanusi ya yaba da babban bankin kasar nan a kan dokar takaita cire kudi
- A ra’ayin tsohon Gwamnan na CBN, tsarin zai fi taba `yan siyasan da ke murde zabe a Najeriya
- Mai martaba ya zargi miyagun ‘yan siyasa da amfani da kazaman kudi domin su cigaba da mulki
Lagos - Mai martaba Muhammad Sanusi II wanda ya rike babban bankin Najeriya tsakanin 2009 zuwa 2014, ya ji dadin sabon tsarin rage yawo da kudi.
A wani jawabi da yayi bayan karatun da ya saba yi, tsohon Sarkin Kano ya fadawa jama’a cewa tsarin da za a fito da shi zai fi yin maganin ‘yan siyasa ne.
Muhammad Sanusi II ya zargi ‘yan siyasa da zaluntar talakawa na tsawon shekaru, idan lokaci zabe ya karaso, sai suyi amfani da kudi domin suyi nasara.
Basaraken yake cewa tsarin da aka fito da shi zai jawo rike kudi ya yi wa ‘yan siyasa wahala, a dalilin haka sai a samu karancin kudin da za ayi magudi.
Za a ga karshen siyasar kudi a 2023?
Sanusi yace bata-garin ‘yan siyasan Najeriya sun saba amfani da dukiya wajen sayen ‘yan daba, jami’an tsaro, malaman zabe da alkalai domin su dade a ofis.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Muhammadu Sanusi II ya ce
"Abin takaici ne yadda mutane za su yi shekara hudu suna kwasar dukiyar al’umma, suna barin mutane a cikin wahala da yunwa, sannan su fito da irin kudaden su sayi kuri’u, su biya 'yan sanda, da DSS, da ma'aikatan INEC da `yan daba a sayo musu kwaya, a saya musu makamai, don hana mutane zabe."
- Muhammad Sanusi II
A rahoton BBC, an ji masanin tattalin arzikin yana cewa wannan tsari da CBN ya fito da shi shi zai fara rage barnar da ake yi wajen tafka magudin zabe.
An yi shekaru 10 da kawo tsarin nan
Khalifan Tijjaniyan yace an yi shekaru goma da soma wannan aiki, an fara tsarin ne a 2012 lokacin shi Sanusi yake rike da kujerar babban banki na kasa.
Tsohon Sarkin yace an kai lokacin da babu dalilin da za a dauki makudan kudi a rika yawo, yake cewa an ga tasirin tsarin nan a lokacin annobar COVID-19.
"Duniya tana canjawa, muna so tsarin kudi a hannun `yan Najeirya ya zama mai sauki, kuma a rage sata...
sai dai zan tuna a lokacin da aka fara, mutane suka yi ta hayaniya cewar ba sa so, amma ga shi yanzu an fara fahimtar amfaninsa."
- Muhammad Sanusi II
'Yan POS za su rasa sana'a
Dazu an rahoto Shugaban kungiyar ‘yan POS a Najeriya, Victor Olojo yana sukar tsarin da ake shirin fito da shi na rage adadin kudin da za su rika yawo.
Victor Olojo yace cigaban mai hakin rijiya za a samu domin ba zai yiwu a ce masu sana’ar POS N20, 000 kurum za su iya cirewa a kowace rana a banki ba.
Asali: Legit.ng