Kwamitin Yaki Da ’Yan Daba Ya Rusa Ofishin Yakin Neman Zaben APC a Zamfara

Kwamitin Yaki Da ’Yan Daba Ya Rusa Ofishin Yakin Neman Zaben APC a Zamfara

  • Wani kwamitin da gwamnan APC a jihar Zamfara ya kafa ya rusa wani ofishin kamfen din APC a jihar
  • An kafa kwamitin ne domin yaki da 'yan daba a jihar da masu tada kayar baya a bangarorin Zamfara
  • Kwamitin ya gargadi 'yan siyasa kan amfani da matasa wajen tada hankalin jama'a a lokutan kamfen da zabe

Gusau, jihar Zamfara - Kwamitin yaki da 'yan daba a jihar Zamfara ta jaddada manufarsa na kakkabe jihar daga 'yan daba da sauran masu tada hankulan jama'a, PM News ta ruwaito.

Bello Bakyasuwa, Shugaban kwamitin, ya ba da tabbacin nan ne a wata tattaunawa da 'yan jarida a birnin Gusau na jihar a ranar Lahadi 11 ga watan Disamba.

Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da kwamitin ya rusa wani ofishin kemfen na APC mai mulkin jihar, tare da cewa ana zargin matasan da ke wurin 'yan daba ne da ke amfani da ofishin a matsayin mafaka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Da sanyin safiyar nan 'yan bindiga suka kone ofishin INEC a wata jiha, uku sun mutu

An rusa ofishin kamfen APC a jihar Zamfara
Kwamitin Yaki Da ’Yan Daba Ya Rusa Ofishin Yakin Neman Zaben APC a Zamfara | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Dalilin da yasa kwamitin ya rusa ofishin APC

Shugaban ya ce mutanen da ke zama a ofishin 'yan ta'adda ne da mutanen banza da kwata-kwata basu cancanci samun mafaka ba a cikin al'umma saboda barnar da suke aikatawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Bisa bayanan sirri da kwamiti na ya samu kan mutanen da ke zama ofishin yakin neman zaben jam'iyyar mun gano suna fakewa domin aikata munanan ayyukansu na ta'addanci da sunan kamfen.
"Mun ma gano wasu kayan sakawa na mata yayin da muka runtuma kame a ofishin."

A wani rahoton TheCable, an ce 'yan daban na amfani da ofishin a matsayin wurin siyar da ababen hawa na sata.

Manufar kafa wannan kwmaitin ba sani ba sabo

Ya ce manufar kwmaitin shine tabbatar da zabe mai ma'ana da babu rikice-rikicen 'yan daba a fadin jihar a 2023.

Kara karanta wannan

Bayan Kashe Ma'kudan Ku'da'de Wajen Gina Gada, Yanzu Dai Gadar Ta Fara Tsagewa

Ya kuma gargadi jam'iyyun siyasa da 'yan siyasa da su guji daukar matasa suna daura su kan turbar dabanci, inda yace hakan na jawo rikici a lokutan zabe.

Gwamna Matawalle ne ya kirkiri wannan kwamiti domin yaki da ayyukan ta'addanci da dabancin siyasa ba tare da la'akari da jam'iyya ba a wata doka da ya samar.

A baya wasu 'yan daba suka lakadawa shugaban 'yan jaridar jihar ta Zamfara duka, lamarin da ya jawo cece-kuce a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.