Gudaji Kazaure Ya Jerowa Garba Shehu Tambayoyi, Ya Yi Karin Bayani a Kan 'Kwamitinsu'

Gudaji Kazaure Ya Jerowa Garba Shehu Tambayoyi, Ya Yi Karin Bayani a Kan 'Kwamitinsu'

  • Muhammad Gudaji Kazaure ya dage cewa Mai girma Muhammadu Buhari ne ya kafa kwamitinsa
  • ‘Dan majalisar tarayyar ya fitar da jawabi wanda ya zama raddi kan hirar da aka yi da Garba Shehu
  • Hon. Gudaji Kazaure ya tabbatar da cewa kwamitin nan yana da goyon bayan shugaban Najeriya

Abuja - Muhammad Gudaji Kazaure ya yi martani ga Malam Garba Shehu, yana mai cewa kwamitinsu halatacce ne, kuma yana mai cin gashin kansa.

Vanguard tace jawabin ‘dan majalisar yana zuwa ne bayan Garba Shehu ya yi watsi da ikirarin Muhammad Gudaji Kazaure ya yi a wata hira da aka yi.

Hon. Muhammad Gudaji Kazaure yake cewa kwamitinsu da yake bincike a kan kudin hatimin da bankuna ke karba ya samu albarkar Shugaban kasa.

‘Dan majalisar ya fitar da jawabi na musamman a ranar Lahadi, yace Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin, kuma ya umarci DSS su taya su yin aikin.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo da Komai Baya, Ya Fadi Gaskiyar Batun Haduwarsa da Gwamnonin PDP

Umarnin da Shugaban kasa ya bada

A cewar Gudaji Kazaure, Mai girma shugaban kasa ya ja-kunne cewa ka da wani daga cikin mukarrabansa ya yi wa aikin kwamitinsu katsalandan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hon. Kazaure yace CP Muhammad Wakili mai ritaya yana cikin ‘yan kwamitin binciken.

Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Jawabin Muhammad Gudaji Kazaure

"Ina so in jawo hankalin jama’a a kan abin da ake ikirarin Malam Garba Shehu ya fada, ya yi watsi da kwamitin da shugaban kasa Buhari ya kafa
An kafa kwamitin ne domin ayi binciken ayyukan babban banki na CBN, sauran bankuna, NIBSS da cibiyoyin kudi.
Ana zaune kalau, bai kamata in yi gardama da Mallam Shehu ba, amma ina so ya zo ya amsa muhimman tambayoyi;
Shin yana nan a lokacin da aka kafa kwamitin? Meyasa aka hana kwamitin yin aiki a karkashin sakataren Gwamnati ko wata ma’aikatar tarayya?

Kara karanta wannan

Ganduje: Dalilin Da Yasa Arewa Ba Ta Da Wani Uzuri Sai Dai Ta Zabi Tinubu

A matsayin ‘Dan Najeriya, babu dokar da ta hana ni yin aikin da shugaban kasa ya bani.
Idan kwamitin bai da hurumin zama, meyasa suke hada-kai da sauran na kusa da shugaban kasa domin a hana ni haduwa da shi (Buhari)?"

- Muhammad Gudaji Kazaure

Binciken Hon. Kazaure

An ji Hon. Kazaure yana cewa kwamitinsu ya binciki kudin da bankuna suka karba tun daga 2013 zuwa shekarar 2020, har adadin ya kai ga tulin Tiriliyoyi.

An rahoto ‘dan majalisar wakilan tarayyar ya nuna akwai zargin an karkartar da Naira tiriliyan 89 da suke cikin asusun babban bankin kasa watau CBN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng