'Yan Najeriya Sun Ci Garabasar Caca Yayin da Wani Yi Hasashen Morocco Za Ta Lallasa Portugal

'Yan Najeriya Sun Ci Garabasar Caca Yayin da Wani Yi Hasashen Morocco Za Ta Lallasa Portugal

  • Wani mutum ya yi hasashe game da wasannin da za a buga na ‘World Cup’ tsakanin kasashen Porgual, Morocco, Faransa da Ingila
  • Mutane da dama sun ga rubutun da ya yi a baya, suka yi masa ba’a a martanin da suka yi kan hasashensa
  • Bayan kammala wasannin, mutane da yawa sun shiga jimami da dana-sanin kin sanya takardun caca kan wannan hasashe da ya tabbata, wasu kuma sun ci miliyoyi

Wani mutum a kafar Twitter, @sportingking365 ya jawo cece-kuce mai girma a kafar sada zumunta bayan da ya bayyana hasashensa kan wasu wasannin kwallo.

A wani rubutun da ya yi a ranar Juma’a 9 ga watan Disamba, mutumin ya ce Morocco za ta lallasa Portugal, kuma Faransa za ta yi nasara kan Ingila a wasannin da za a buga a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Duk da Kyauna, “Samarin Shaho” Guduna Suke yi, Budurwa Mai Kamun Kai Tayi Bayani

Yadda 'yan Najeriya suka kwashi garabasar caca
'Yan Najeriya Sun Ci Garabasar Caca Yayin da Wani Yi Hasashen Morocco Za Ta Lallasa Portugal | Hoto: @kydr001, @dizboicole
Asali: UGC

‘Yan Najeriya sun kwashi garabasar caca

Yayin da ya yada rubutun, mutane da yawa sun ce wasa yake kuma bai san me yake ba, tare da bayyana mamakin ta yaya kasa kamar Morocco ta ci kasa kamar ta su Ronaldo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai da, baya ga lallasa Portugal da Morocco ta yi, Faransa ta kori Ingila daga gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Qatar.

Kwatsam bayan tabbatar hasashensa, rubutun mutumin ya yadu ainun a kafar sada zumunta, inda mutane ke ta’ajibin abin da ya faru, wasu kuwa tuni suka lashi romon miliyoyi saboda sun saka caca a wasannin.

Ga abin da ya rubuta:

Martanin jama’a

Jama’ar da dama sun yi martani kan wannan lamari, ga dai kadan daga abin da muka tattaro muku daga shafin twitter:

@stakewisee:

“Na ci wannan wasan nima.”

Kara karanta wannan

Dala 500k/N220m: Tulin miliyoyin da dan Najeriya ya kai banki zai ajiye ya girgiza jama'a

@BusyBrain202:

"Ina cikin wadanda suka yi nasara nima."

@betwin_247:

"Yanzu aka bani bani 10.5m na Disamba. Zan ba da 500k ga mutum 100 na farko da suka yada wannan rubutun.”

@aystickz:

"Nagode Allah da naga wannan tun farko. Nagode mutumina, na ci N5.7m.”

@OlayiwoleIsaac:

"Ina taya ka murna baba sabon sarki mai tasowa. Mun san wadancan da ke ciyar da jama’a a titi. Ko da ka gani ba za ka yi wasa da shi da karfi ba. Ina taya attajiran yaran da suka buga murnan cin nasara.”

@carefulWealth:

"Nagode 1.3m.”

@Theopulenceman:

“Mutumin da ya hango gobe kenan.”

Kwanakin baya 'yan kwallon kasar Saudiyya suka lallasa su Messi; Argentina, sun kwashi garabasa daga gwamnatin Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.