'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake Mai Ƙima a Jihar Zamfara
- Allah ya yi wa hakimin Yankuzo a jihar Zamfara, Alhaji Hamza Abdullahi Kogo, rasuwa ranar Asabar 10 ga watan Disamba, 2022
- Basaraken ya rasa rayuwarsa sanadiyyar raunukan da ya samu yayin da 'yan bindiga suka farmake shi ranar Jumu'a
- Mazauna yankin da marigayin ke jagoranta sun ce ba su taba ganin harin 'yan bindiga a yankinsu ba tun farkon matsalar
Zamfara - Yan bindigan daji sun kashe hakimin Yankuzo, Alhaji Hamza Abdullahi Kogo, na masarautar Tsafe a jihar Zamfara.
Channels tv ta rahoto cewa 'yan ta'addan sun farmaki Basaraken ne yayin da yake kan hanyar komawa yankinsa daga wani taro da ya halarta ranar Jumu'a da misalin karfe 8:00 na dare.
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa maharan sun harbi Basaraken kuma ya samu raunuka sosai lokacin da suka yi yunƙurin garkuwa da shi.
Daga nan aka garzaya da shi babbar Cibiyar lafiya ta tarayya dake Gusau, babban birnin jihar daga baya Allah ya masa cikawa ranar Asabar da daddare.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Garin Yankuzo nan ne mahaifar hatsabibin ɗan ta'addan nan, Ado Aleiru, wanda Masarautar Yandoton Daji ta naɗa masa rawanin Sarauta a watan Yulin wannan shekara da muke ciki.
Da yawan mazauna garin Yankuzo sun bayyana cewa garinsu bai taɓa fuskantar harin 'yan bindiga ba tun da aka fara fama da matsalar 'yan fashin jeji a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya.
Har zuwa yanzun da muka kawo muku wannan rahoton, hukumomin tsaro a jihar ba su ce komai game da kisan babban basaraken ba, Lindaikejiblog ta rahoto.
A watannin da suka shige mataimakin gwamnan Zamfara, Sanata Hassan Nasiha, yace shirin tattaunawar lafiya da 'yan ta'adda ta fara haifar da ɗa mai ido a kokarin dawo da zaman aminci a jihar.
Sai dai kuma bayan haka, hukumomin soji sun ci gaba da kai zafafan hare-hare ta sama da ƙasa kan sansanonin 'yan ta'adda jihar da ma sauran jihohin arewa maso yamma da lamarin ya shafa.
Kansila da Wani Mutum Guda Sun Mutu a Wani Rikicin Kabilanci a Ondo
A wani labarin kuma Wasu matasa ɗauke da bindigu sun kashe Kansila da Wani mutum ɗaya yayin wani rikici a jihar Ondo
Bayanai sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne tun tale-tale tsakanin manoman Oyo/Osun mazauna yankin Odigbo da kuma iyalan Oluku na Ikale.
Kwamandan Amotekun ya tabbatar da mutuwan kansilan yankin da wani mutum ɗaya yayin harin da ake zargin matasan Ikale da kaiwa.
Asali: Legit.ng