Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Bindiga a Zamfara, Sun Kwamushe Mutum 9
- Wasu tsagerun da ke harkalla da ‘yan bindiga sun shiga hannun jami’an tsaro a kwanakin da suka gabata
- Rundunar ‘yan sanda ta dakile harin ‘yan bindiga a Zamfara, sun kuma wasu mutane da dama
- Jihohin Arewa maos Yammaicn Najeriya na fuskantar barazanar hare-haren ‘yan bindiga, ana samun sauki
Gusau, jihar Zamfara - ‘Yan sandan jihar Zamfara sun yi nasarar dakile harin ‘yan ta’adda har sau biyu a kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi na jihar.
Wannan na fitowa ne daga bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Muhammad Shehu yayin da yake gabatar da masu aikata laifuka a ranar Asabar a birnin Gusau ta jihar Zamfara.
A cewar sanarwar da Channels Tv tace ta samo, ‘yan sanda sun kama masu kai bayanan sirri ga ‘yan bindigan, wadanda ake zargin sun hada kai wajen kakaba haraji ga mazuana tare da lalata kokarin jami’an tsaro a yankin.
Hakazalika, rundunar ta ce ta kama wasu abokan harkallar ‘yan bindiga mutum shida da suka kware wajen harkallar miyagun kwayoyi da ‘yan bindiga a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Su wa aka kama da yadda aka kama su
Wadanda aka kaman sun hada da Abubakar Idaho mai shekaru 75 na kauyen Kwarya Tsugunne a karamar hukumar Maru da Almustapha Dahiru mai shekaru 69 na kauyen Yanbuki da ke karamar hukumar Zurmi.
An kama su ne bisa zargin hada hannu da ‘yan bindigan da suka kakaba haraji kan jama’ar kauyukansu da ke jihar ta Zamfara.
Mutum na uku da aka kama shine Muhammad Jibrin na kauyen Kekun Waje a karamar hukumar Bungudu da ke kai wa ‘yan bindiga bayanan motsin jami’an tsaro a kauyensu.
Shehu ya kuma bayyana cewa, jami’an tsaro yayin aikin sintiri a kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi sun samu kiran gaggawa na shirin farmakin ‘yan bindiga a wasu kauyuka a kananan hukumomin biyu.
Matar Tinubu Tace Nan Gaba Za'ai Takarar Kirsita da Kirsita, Amma Yanzu Lokacin Muslmi Da Musulmi Ne
An fafata tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga
Ya ce ‘yan sanda sun yi aiki cikin tsanaki, inda suka dakile harin da ‘yan bindigan suka kawo yayin wata kwarya-kwaryar fafatawa da suka yi da ta kai sa’a guda, Ripples Nigeria ta ruwaito.
Sauran mutum shida aka kama an kwamushe su ne yayin da suke kokarin shigar da wani busasshen ganje mai kama da tabar wiwi da aka ce sun dauko daga Legas zuwa Shinkafi.
Hakazalika, an kama wani da ya dauko tabar wiwi, inda ya nufi kai wa ga wasu a karamar hukumar Kaura Namoda a jihar ta Zamfara.
Sanarwar ta kuma bayyana kayayyakin da aka kwato da suka hada makamai, miyagun kwayoyi, Babura da mota da dai sauran kayayyakin aikata laifuka.
Ya zuwa yanzu dai ‘yan sanda na ci gaba da bincike, za kuma a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala cikakken bincike.
Jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da samun nasara kan tsageru, a makon da ya gabata ne suka ceto mutum uku da 'yan bindiga suka sace a babban birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng