Gwamna Zulum Ya Yi Alkawarin Kawo 95% Na Kuri’un Jihar Borno Ga Tinubu a 2023
- Gwamnan jihar Borno ya bayyana shirinsa na kawo kuri’i ga Bola Tinubu da Shettima a zaben 2023 mai zuwa
- Babagana Zulum ya ce zai samar da kaso 95% na kuri’un jihar Borno ga Tinubu a zaben na 2023 mai zuwa
- Ya kuma bukaci a dama da matasa tare da samar musu ababen more rayuwa da tallafi a yankin Arewa maso Gabas
Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi alkawarin kawo kuri’un jiharsa ga jam’iyyar APC a zaben 2023 na shugaban kasa.
Gwamnan ya yiwa abokin takarar Bola Ahmad Tinubu, Kashim Shettima wannan alkawarin ne yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar 10 ga watan Disamba yayin zantawa da tawagar kamfen na mata da Sanata Oluremi Tinubu ta jagoranta, Vanguard ta ruwaito.
Matar Tinubu, Oluremi ta jagoranci tawagar mata ne zuwa jihar Borno domin kaddamar da kamfen din takarar shugaban kasa na Tinubu sashen mata a Arewa maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Zulum ga tafiyar Tibubu da Shettima:
“Bani da wani zabin da ya wuce na kawo kur’un jihar ga Tinubu/Shettima da ma daukar APC baki daya. Ba zan ba shi (Kashim Shettima) kunya ba."
Zulum ya tuna yadda Shettima ya karrama shi ta hanyar ba shi matsayin shugaban makaranta tare da nada shi kwamishina a lokacin da yake gwamna.
Hakazalika, Zulum ya ce ya yaba yadda Shettima ya dauko shi a matsayin wanda ya gaje shi a lokacin da ya bar mulkin Borno.
Ya kara da cewa:
“Za mu yi aiki tukuru wajen tabbatar kawo kaso 95% na kuri’u ga APC.”
A dama da matasan Arewa maso Gabas
Sai dai, ya bukaci tawagar ta mata mai gangamin Tinubu/Shettima da ta san yadda za ta dama da matan Arewa maso Gabas, musamman kan fannin da ya shafi ilimi da daidaiton jinsi.
Yayin kaddamar da gangamin, matar Tinubu; Oluremi da matar Shettima Nana sun yi alkawarin aiki tare wajen habaka ilimin ‘ya’ya mata tare da tabbatar da samar da hanyoyin tallafawa matasa a yankin.
Sanata Oluremi ta ce gwamnatin Tinubu za ta ba mata da matasa muhimmanci da kulawa ta musamman a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar samar da sana’o’i don ci gaban al’umma.
A cewarta, akwai bukatar sake fasalin tsarin matasa tare da mai dasu masu amfanar kansu ta hanyoyi maso fa’idar gaske.
A jihar Kano kuwa, APC da NNPP na ci gaba da musayar yawo, dan takarar gwamnan NNPP ya ce Kanawa sun gaji da mulkin molon ka da gwamna Ganduje ke yi.
Asali: Legit.ng