Babban Abin Kunya Yayin Da Kotu Ta Kori Dukkan Ciyamomi Da Kansilolin APC A Shahararriyar Jiha
- Babban kotun tarayya ta kori ciyamomi 13 da kansiloli 171 a jihar Ebonyi a ranar Juma'a 9 ga watan Disamba
- Hakan ya faru ne yayin da Mai Shari'a Fatun Riman ya yi hukuncin cewa zaben da ya samar ciyamomin da kansilolin ba bisa doka aka yi shi ba
- Wannan hukuncin ya haifar da murna da farin ciki a bangaren wanda ya shigar da kara, Mudi Erhenede wanda ya yi wa kotun godiya
Abakalili, Ebonyi - Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abakaliki ta soke zaben karamar hukumar Ebonyi ta kori ciyamomi 13 da kansiloli 171, The Nation ta rahoto.
Mai shari'a Fatun Riman wanda ya yi shari'a a ranar Juma'a, 9 ga watan Disamba, ya bada umurnin a kwace dukkan kudin wata-wata da gwamnatin tarayya ke bawa ciyamomin har zai an zabi halastattu.
Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kotun ta yanke wannan hukuncin ne kan cewa zaben da hukumar zabe mai zaman kanta na jihar (EBSIEC) ta yi a ranar 31 ga watan Mayu ba bisa ka'ida bane.
Martanin wanda ya shigar da kara
A bangarensa, Mudi Erhenede, wanda ya shigar da kara ya bayyana farin cikinsa kan hukuncin kotun.
"A hukuncin yau, kotu ta yarda cewa babban kotun jihar Ebonyi ba ta da ikon soke hukuncin da kotun tarayya ta yi domin ita ba kotun daukaka kara bane.
"Wadannan mutanen da ke gabatar da kansu a matsayin ciyamomi ba bisa ka'ida suka hau kujerun ba.
"Wani ne kawai ya nada su. A cikin wadanda aka yi kara akwai CBN, Antoni janar na tarayya, da ma'aikatar kudi."
Ebonyi: Kotu ta sallami shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jiha daga takarar 2023
Babban kotun tarayya mai zamanta a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi ta sallami shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, Honarabul Victor Chukwu, daga matsayin dan takarar APC na mazabar Ezza ta arewa maso yamma.
A baya, dan majalisar yana jam'iyyar Peoples Democratic Party ne kafin daga baya ya fita ya shigo APC tare da Gwamna David Umahi na jihar, rahoton Vanguard.
Victor Chukwu ya rasa takararsa ne saboda takkadama da ta biyo bayan zaben cikin gida tare da rashin sahihancin kasancewarsa mamba na APC.
Asali: Legit.ng