Kiwon Lafiya: Hanyoyi 4 na kauracewa warin baki
Warin baki cuta da ka iya kama kowa, sai dai ance babu wata cuta da ba a iya magance ta. Da yawa daga cikin mutane masu fama da warin baki, shiga cikin abokai ko 'yan uwa yana yi musu wahala, sanadiyar janyo musu barazanar jin kunya ko kuma su na magana ana toshe hanci.
Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa warin baki abu da duka wanda ke dauke da shi, to ko shakka babu shi ya gadarwa kansa wannan wari na baki, sanadiyar rashin tsaftace baki ko kuma rashin kula wajen ciyaye na abinci da ka iya janyo cutar.
Akwai nau'ukan abinci wanda da zarar mutum ya yi amfani dasu suke sauya launin baki, baya ga haka akwai lokuta da ba su dace a ci wasu nau'ukan abincin ba, kamar irin su shan abin mai zaki kafin kwanciyar bacci.
Ga jerin tafarki hudu da ka iya taimakawa wajen kawar da warin baki dake addabar mutane da dama, ta yadda ba su iya shiga mutane.
1. Yin amfani da lemun bawo musamman ma lemun tsami, domin su na tattare da sunadarai dake hana kwayoyin cututtuka na cin baki dake janyo warin na baki.
Bincike ya nuna cewa, zuba bari guda na lemun tsami a cikin kofi daya na ruwa, sannan a dan gauraya da gishiri wanda bai wuci rabin cokalin shan shayi ba, kuma a kurkura a baki kafin kwanciyar bacci, yana hana warin baki.
2. Garin Khal na itacen tufa
Gauraya cokali daya na garin khal na itacen tare da kofi daya na ruwa kuma a kwankwade yana hana warin baki.
KU KARANTA: Gargadi daga Buratai: Mazauna yankin Biyafara ku kula da kawowa zaman lafiya cikas
3. Garin hodar gashin burodi: Bayan fitar da hakora da kara musa haske tar-tar, idan aka kwaba garin hodar gashin burodi da ruwan dumi aka kurkura a baki koda sau biyu a rana, tabbas mutum zai yi sallama da warin baki
4. Ruwan shayi zalla babu madara ko kuma shayi na koren ganye na daukewa masu sha warin baki.
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng