Hotuna Masu Ban Sha'awa Sun Bayyana Yayin Da Ɗan Buratai Ya Tuƙa Shi A Jirgin Sama Daga Sokoto Zuwa Abuja

Hotuna Masu Ban Sha'awa Sun Bayyana Yayin Da Ɗan Buratai Ya Tuƙa Shi A Jirgin Sama Daga Sokoto Zuwa Abuja

  • Tukur Buratai, tsohon COAS, ya yi matukar murna da alfahari yayin da dansa ya tuka shi daga jirgin Arik Air a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba
  • Ta shafinsa na Facebook, tsohon shugaban sojojin na Najeriya ya ce dansa ne ya tuka shi daga Sokoto zuwa Abuja
  • Buratai ya ce dansa da wani kyaftin, Ahmed Musa, sune matukan jirgin da suka tuka su zuwa Abuja, kuma ya musu addu'a

Tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, COAS, Tukur Buratai ya bayyana farin cikinsa bayan dansa, Tukur Buratai Jnr, a baya-bayan nan ya tuka shi a jirgi daga Sokoto zuwa Abuja.

Da ya ke wallafa hotunsa tare da dansa da dayan matukin jirgin, Ahmed Musa, Buratai ya bayyana cewa ya yi alfahari da lamarin.

Buratai
Kyawawan Hotuna Sun Fito Yayin Da Ɗan Buratai Ya Tuƙa Shi A Jirgin Sama Daga Sokoto Zuwa Abuja. Hoto: Tukur Buratai
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Cikin murna ya ce dansa da dayan matukin jirgin, Kyaftin Ahmed Musa, sun dace yadda ake so.

Tsohon shugaban sojojin, ya rubuta a Facebook cewa:

"Babban rana ta 8 ga watan Disamban 2022 da da na Tukur Buratai Jnr ya tuka ni a jirgin Arik Air daga Sokoto zuwa Abuja. Na yi alfahari sosai. Sun dace da kyaftin dinsa Ahmed Musa. Ma'aikatan jirgin suna da ladabi sosai. Allah ya albarkace ku duka."

Jigon jam'iyyar All Progressives Congress APC, Mr Joe Igbokwe shima ya wallafa wannan hotunan a shafinsa na Facebook yana mai taya Buratai murna da fatan alheri.

Martanin wasu yan Najeriya a Facebook

Anas Sa'idu ya ce:

"Masha Allah, Allah ya cigaba da maka jagora da kiyaye iyalinsa."

Haruna Idris Zaria ya ce:

"Ya Allah yabada saa, kuma Ya kara arziki da daukaka amin."

Beyidi Martins ya ce:

"Ina taya ka murna sir. Allah ya sa ka cigaba da amfana da romon hidimar da ka yi."

Buratai Ya Bayyana Jam'iyyar Da Za Ta Yi Nasara A Zaben Najeriya Na Shekarar 2023

A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojojin kasan Najeriya, Laftanant Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya ce yana ganin jam'iyyar APC mai mulkin kasa ita ce za ta lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta rahoto cewa Buratai yana cikin wadanda suka halarci babban taron da matasan jam'iyyar APC suka yi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel