Matakai, Abubuwa Da Ake Buƙata Don Neman Aiki A Hukumar Tsaro Ta NSCDC A Shekarar 2022/2023
Hukumar tsaro na Najeriya, NSCDC, ta sanar da cewa za ta bude shafinta na yanar gizo na daukan aiki daga ranar Litinin, 12 ga watan Disamba.
An fitar da sanarwar fara daukan sabbin ma'aikatan ne ta shafin yanar gizo na NSCDC.
Kazalika, hukumar tana sanar da duk masu sha'awan neman aiki cewa rajistan neman aikin kyauta ne.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yana kuma da muhimmanci a san cewa za a iya samun fom din a intanet kuma dukkan abin da za a yi na neman aikin a yanar gizo ne.
Ga jerin matakan da za a bi don neman aikin:
1. Ziyarci shafin NSCDC: Masu son neman aikin su ziyarci shafin hukumar a www.nscdc.gov.ng ko cdfipb.careers domin karanta dukkan umurni, dokoki da abubuwan da ake bukata don neman aikin.
2. Latsa 'apply': Bayan mai neman aikin ya karanta umarnin da aka bayar a shafin yanar gizon, ana umartan shi da ya danna kan alamar APPLY don ci gaba.
3. Shigar da bayanan rayuwa: Wannan shine matakin da za a fara cike baynai gadan-gadan kuma dole a cike su yadda ya dace. Wasu daga cikin bayanan sun hada da cikakken suna, ƙasa ta asali, jinsi, lambar shaidar dan ƙasa, da wasu da dama.
4. Dora takardun shaidarka da katin shaidar dan ƙasa: A ƙarshen cike fom din, za a nemi masu neman aiki su ɗora takardar shaidar karatunsu da takardar shaidar zaman dan ƙasa.
5. Ka turo fom din neman aikin: Wannan shi ne mataki na ƙarshe. Abin da ake buƙata daga mai nema shi ne danna maɓallin aikawa bayan ya tabbatar duk bayanan da aka cika daidai ne.
Abubuwan da ake bukata don daukan aikin Civil Defence na 2022
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku
Tsawo (Maza) - 1.68m
Tsawo (Mata) - 1.65m
Shekara - 18-30
Karatu - Digiri (BSc), HND ko OND, WASSCE
Dalibai masu hazaka 4 da suka ci jarrabawarsu ta WAEC 2022 da sakamakon A
Hukumar shirya jarrabawa kammala babban sakandare a Afirka ta yamma, WAEC, ta fitar da sakamakon jarrabawa na shekarar 2022.
Wannan jarrabawar na da muhimmanci domin shine manuniya ga yadda karatun dalibi za ta kasance a gaba, don sai da shi ake zuwa jami'a ko kwalleji da sauransu.
Asali: Legit.ng