Wani Dan Najeriya Ya Janyo Cece-Kuce Yayin da Ya Kwashi Tsabar Kudi Dala Dubu 500 Zuwa Banki

Wani Dan Najeriya Ya Janyo Cece-Kuce Yayin da Ya Kwashi Tsabar Kudi Dala Dubu 500 Zuwa Banki

  • Hotunan wani dan Najeriya da ya kwashi kudade $500,000 (N220m) zuwa banki ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta
  • Mutumin da ba a bayyana sunansa ba ana kyautata zaton ya kawo kudaden ne zuwa banki yayin da Najeriya ta sauya fasalin Naira
  • Jita-jitan da ke yawo na cewa, kasar Amurka za ta daina amfani da wasu daga cikin kudadenta na ci gaba da jawo magana a duniya

Najeriya - Wani dan Najeriya ya cece-kuce yayin da ya dauko tulin kudade $500,000, da suka yi daidai Naira miliyan 220 zuwa banki domin ya ajiye.

Hoton mutumin da ba a bayyana wanene shi ba ya yadu a kafar sada zumunta, inda mutane da dama ke ta mamaki tare da rokon Allah su ma ya basu.

An dauki hoton ne a daya daga cikin bankunan kasar nan, wasu mutane sun shiga mamakin dalilin da yasa mutumin ya ajiye kudade masu yawa kamar wadannan.

Kara karanta wannan

Manufofin Babban Bankin Kasa Akan Fitar Da Kudi Tauyewa 'Yan Nigeria Hakk'ine – Masanin Kudi, Muda Yusuf

Mai kudi ya jawo cece-kuce a Najeriya bayan kudadensa banki
Wani Dan Najeriya Ya Janyo Cece-Kuce Yayin da Ya Kwashi Tsabar Kudi Dala Dubu 500 Zuwa Banki | Hoto: Lara Wise
Asali: UGC

Bai bayyana ko mutumin ya saba ka’ida da dokar adana kudi ta Najeriya ba kasancewar ya adana kudi da yawa gashi kuma ana karancin dala a kasar, lamarin da ya karya Naira.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Najeriya dai na ci gaba da kawo dokokin ajiye da cire kudi a kokarin da take na farfado da tattalin arzikinta.

Martanin jama’a

Wani yace::

"Kada ku yi masa hassada mana. Kuka san ko mai garkuwa da mutane ne, dan bindiga ko dan ta’adda? Su ne masu rike da kudade musamman daloli a yanzu.”

Wani kuma cewa ya yi:

“Ku ci gaba da bulayi. Kudaden da kuka sa wani ya ajiye muku a asusun da ya yi bacci kuma kuna umartarsa ya dauki hoton shaidar ajiye kudin.”

A kwanakin baya, yawaitar siyan daloli a kasar bayan fage na kadan daga cikin dalilan da suka darajar Naira ta yi kasa a duniya.

Kara karanta wannan

Matashin Miloniya Ya Baje Kolin Hadadden Gidansa da Tsadaddiyar Motar Benz, Bidiyon Ya Yadu

Wani mai sharhi a yi imani da cewa, yawaita boye dala ko kuma sauya Naira zuwa dala na ci gaba da cike kasuwannin bayan fage a kasar nan.

Abbas Yishau, wani dan jarida a gidan rediyon Now in Kano ya shaidawa Legit.ng cewa, da yawan masu boye kudaden nan sun shiga tsoron nan gaba za a daina amfani da wasu daga nau’in dala a duniya.

A makon nan gwamnan CBN ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya kan batun da ya shafi kayyade adadin kudaden da 'yan kasar za su iya cirewa a kowacce rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.