Wani Mai Sayar da 'Ice Cream' Ya Bar Wurin Kasuwanbi, Ya Bi Wata Budurwa A Bidiyo

Wani Mai Sayar da 'Ice Cream' Ya Bar Wurin Kasuwanbi, Ya Bi Wata Budurwa A Bidiyo

  • Wani mai sayar da daskararriyar Madara 'Ice Cream' ya bar wurin sana'arsa kana ya bi wata budurwa da ta gayyace shi
  • A wani bidiyo da ya karaɗe soshiyal midiya, an hangi lokacin da mutumin ya bar wurin kasuwancin ya bi matar
  • Abin da mai sayar da madarar ya yi ya ja hankali da haddasa cece-kuce tsakanin ma'abota amfani da TikTok

Mutane sun bayyana ra'ayoyinsu game da wani Bidiyo da aka ga wani mutumi ya bar wurin kasuwancinsa ya bi mace.

Mutumin, wanda ke sana'ar sayar da daskararriyar madara 'Ice Cream' ya bi budurwar ne a wani Bidiyo da Omapearl ta wallafa a shafinta na TikTok.

Mai Ice Cream.
Wani Mai Sayar da 'Ice Cream' Ya Bar Wurin Kasuwanbi, Ya Bi Wata Budurwa A Bidiyo Hoto: @omapearl
Asali: UGC

A cikin ɗan taƙaitaccen bidiyon da bai wuce dakika 57 ba, budurwar ta je wurin mutumin yayin da yake sauraron kwastomominsa.

Da zuwa ta miƙa masa wata 'yar ƙaramar takarda mai ɗauke da sakon gayyatarsa zuwa makwancinta, daga nan kuma ta ruga da gudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin sha'awa da ban mamaki, ba tare da ɓata lokaci ba mutumin ya bar wurin Ice Cream ɗin kana ya bi bayan matashiyar budurwar.

Abinda mutumin ya yi dai ya bar masu sayen Ice Cream a wurin baki buɗe yayin da suka tsaya a wurin suna kallon abin mamaki.

Bidiyon dai ya tara ra'ayoyin mutane daban-daban sama da 1,500 a shafin sada zumunta TikTiko.

Kalli Bidiyon anan

Mutane sun maida martani kan lamarin

Chris Okpata ya ce:

"Wannan fa ba zai iya ba."

Lamkaysamz ya tambayi cewa:

"To wai wa ya barwa abinda yake sayarwa?"

Dexzyboss ya ce:

"Saura kiris na ji wa kaina rauni yayin da runtuma da gudu sashin bayyana ra'ayoyi."

Mutumi Ya Koka Kan Yadda Ɗansa Ya Hana Shi Kwanciya da Matarsa, Bidiyon Ya Ja Hankali

A wani labarin kuma Wani Magidanci ya wallafa bidiyon yadda ɗansa ya hana shi rawar gaban hantsi wajen jin daɗi da matarsa

A bidiyon wanda ya hadda cece-kuce a soshiyal Midiya, mutumin ya nuna yadda a ko da yaushe matar take kwanciya da ɗan, ta hana shi hawa gadon baki ɗaya.

Ganin yadda lamarin ke ƙara ta'azzara, magidancin ya roki ɗan karamin yaron ya tausaya masa ya koma kan ƙaramin gadon da aka tanadar masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel