2022 World Cup: Gwamnatin Qatar tace Zina haramun ne, duk wanda aka kama zai shiga Kurkuku

2022 World Cup: Gwamnatin Qatar tace Zina haramun ne, duk wanda aka kama zai shiga Kurkuku

  • Gwamnatin kasar Qatar tace a gasar kwallon kafar duniya ta bana, ba zata yarda da fasadi da lalaci ba
  • Qatar kasar Larabawa ce kuma an kafa dokoki haramcin Zinaa, shaye-shaye da casu ga kowani mutum
  • Kwamitin koli da ta shirya gasar ta bayyana cewa ko kadan ba za'a canza dokokin addini don gasar kwallo ba

An gargadi masu niyyar halartan gasar kwallon duniya da za'a yi a kasar Qatar bana cewa duk wanda aka kama kebance da wani wanda babu aure tsakaninsu zai iya shiga kurkukun shekaru bakwai.

Hakazalika an hana shan giya a bainar jama'a kamar yadda ake yi a wasu kasashe.

Gwamnatin kasar Larabawar ta Qatar ta bayyana cewa ko kadan ba zata canza dokokinta na addinin Islama ba don wani gasar kwallo.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Bidiyon Da Hotunan Yadda Sabuwar Gada Ta Rufta Da Jami'an Gwamnati Yayin Bikin Kaddamarwa a DRC

Hukumomi a kasar Birtaniya sun fara kokawa kan yiwuwar takurawa yan kasarta dake niyyar zuwa Qatar kallon wasannin kwallon.

Qatar
2022 World Cup: Gwamnatin Qatar tace Zina haramun ne, duk wanda aka kama zai shiga Kurkuku
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata majiya ta yan sanda ta bayyanawa DailyStar cewa:

"Idan ba miji da mata masu aure ba, basu yarda mutum yayi jima'i ba. Hakazalika babu casu gaba daya. Kowa ya fahimci haka ko kuma a jefashi kurkuku."
"Yan kallo su shirya, babu jima'i da zinace-zinace wannan karon."

Zina da luwadi haramun ne a kasar Qatar, kuma duk wanda aka kama zai iya kwashe shekaru 7 a daure.

Shugaban kwamitin tsare-tsaren gasar kwallon FIFA 2022 World Cup, Nasser Al-Khater, ya bayyana cewa:

"Abinda yafi muhimmanci garemu shine tsaron lafiyar kowani dan kallo. Amma rungume-rungume ba al'adarmu bace - kuma wannan ya shafi kowa."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: