'Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Jihar Anambra, Sun Yi Awon Gaba Da Jarirai
- Yan bindiga sun sace jarirai sabbin haihuwa a Asibitin haihuwa dake garin Nkpologwu, ƙaramar hukumar Aguata a jihar Anambra
- Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne ranar Talata da daddare, babu sahihin bayani kan dalilin sace jariran har yau
- Jihar Anambra dake shiyyar kudu maso gabashin Najeriya na fama da ayyukan yan bindiga da 'yan aware
Anambra - Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kar farmaki Asibitin haihuwa dake garin Nkpologwu, ƙaramar hukumar Aguata a jihar Anambra, sun kwashi jarirai sabbin haihuwa huɗu.
Jaridar Punch tace har yanzun ba'a gano sababin wannan rashin imani ba amma wata majiya a yankin ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai ranar Laraba.
Duk da babu cikakken bayani kan iya ɓarnar da maharan suka tafka, mazauna garin sun ce lamarin ya faru da daren ranar Talata amma mutane sun samu labari ran Laraba.
Majiyar tace, "Ya faru a garinmu ranar Talata da daddare kuma mutane na ta magana a kai tun ranar Laraba da safe. Sun ce yan bindiga suka kutsa Asibitin suka ɗauki jarirai huɗu."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Daga bayanan da na samu a bakin mazauna yankin babu wanda ya jikkta sanadin harin kuma babu wanda aka kashe. Dalilin kai harin dai ba'a sani ba har yanzun."
"Wasu na cewa sun kwashi jaririn ne domin su sayar da su ga marasa haihuwa, wasu kuma na faɗin zata iya yuwuwa asirin kuɗi zasu yi da su."
Bamu da labarin harin - Yan sanda
Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Anambra, DSP Ikenga, yace hukumarsu ba ta da masaniya kan harin amma zai bincika.
A rahoton Vanguard, Ikenga yace:
"Bani da rahoto makamancin haka a Ofishina yanzu haka amma zan bincika sannan na dawo gare ku."
A wani labarin kuma Jiragen Yakin Soji Sun Ragargaji Yan Bindiga a Kananan Hukumomi 3 Na Jihar Kaduna
Rundunar sojin sama ta ƙara samun nasarar sheke yan ta'adda a hare-haren bama-bamai da jiragenta ke kaiwa sansanoninsu a jihar Kaduna.
A wata sanarwa da gwamnatin Kaduna ta fitar, tace jiragen yaki sun kakkaɓe yan bindiga a yankin ƙananan hukumomi 3 dake jihar.
Asali: Legit.ng