Basaraken da Aka Sace a Ondo, Oba Clement Omoola Jimoh Ya Shaki Iskar ’Yanci da Hannun ’Yan Bindiga

Basaraken da Aka Sace a Ondo, Oba Clement Omoola Jimoh Ya Shaki Iskar ’Yanci da Hannun ’Yan Bindiga

  • Miyagun ‘yan bindigan da suka sace wani basarake a jihar Ondo sun sako shi a jiya Laraba 7 ga watan Disamba
  • A makon da ya gabata ne aka sace basaraken, inda aka kutsa har cikin gida aka yi awon gaba dashi
  • ‘Yan bindiga sun nemi fansan miliyoyin kudade, ya zuwa yanzu dai ba a san ko fansa aka biya aka sako shi ba

Akoko, jihar Ondo - Basaraken gargajiya da aka sace a makon jiya a jihar Ondo, Oloso na Oso Ajowa a karamar hukumar Akoko North West ya shaki iskar ‘yanci.

Oba Clement Omoola Jimoh ya dawo gida ne bayan da ya shafe kwanaki bakwai a hannun ‘yan bindiga, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

A cewar wata majiyar kusa da basaraken, an sako shi ne a ranar Laraba 7 ga watan Disamba, inda ta kara da cewa, yanzu haka yana asibiti ana duba lafiyarsa.

Sai dai, ba a bayyana sunan asibitin da basaraken yake kwance ba.

'Yan bindiga sun sako basaraken da suka sace a Ondo
Basaraken da Aka Sace a Ondo, Oba Clement Omoola Jimoh Ya Shaki Iskar ’Yanci da Hannun ’Yan Bindiga | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda aka sace basaraken

A makon da ya gabata ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka kutsa gidan basaraken tare da yin awon gaba dashi zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami ya tabbatar da faruwar lamarin ga kafar labarai ta Channels Tv ta wayar tarho.

An ce ‘yan bindigan sun nemi a basu kudaden da sauka kai N100m a matsayin kudin fansa, daga baya suka rage zuwa N10m, Punch ta ruwaito.

Ya zuwa yanzu dai ba a san ko kudin fansa aka biya kafin a sako basaraken ba ko kuma sun sake shi bisa radin kansu.

An sha yin awon gaba da sarakunan gargajiya a Najeriya, lamarin da ke kaiwa ga biyan kudin fansa da yawa.

'Yan bindiga sun sace sarki a jihar Filato, sun kutsa har cikin gida

A wani labarin kuma, kunji yadda wasu tsagerun 'yan bindiga suka kutsa har gida suka yi awon gaba da wani sarki a jihar Filato.

An sace Mai Martaba Dauda Mohammed Suleiman bayan da 'yan bindiga suka shiga har fadarsa a Pinau suka yi barna.

Wani mazaunin garin ya shaidawa Punch cewa, an bazama neman sarkin da fatan za a same shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel