Hukumar Kwastam Ta Kame Tireloli 73 da Aka Shigo Dasu Najeriya Makare da Shinkafar Waje
- Hukumar kwastam ta yi nasarar kame wasu haramtattun kayayyaki a bakin iyaka ta Idiroko a jihar Osun
- An kama tireloli akalla 73 da aka ce sun zo makare da shinkafa ‘yar kasar waje da aka kawo Najeriya
- Gwamnatin Buhari ta haramta shigo da shinkafar waje, lamarin da yasa ake yin fasa-kwabrinta
Idiroko, jihar Ogun - Hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) a jihar Ogun ta yi nasarar kame tireloli 73 na haramtacciyar shinkafar kasar waje da sauran haramtattun kayayyaki da kudinsu ya kai N4.8bn.
Kwanturolan hukumar a jihar, Bamidele Makinde ne ya bayyana hakan a Idiroko yayin da yake yiwa ‘yan jarida bayanin ayyukan da hukumar ta yi kwanan nan, TVC News ta ruwaito.
A cewarsa, sama da buhunnan shinkafar waje 44,000 ne aka kama da aka shigo dasu daga jamhriyar Benin tsakanin 6 ga watan Fabrairu zuwa 6 ga watan Disamban 2022.
Ya yi bayanin cewa, an kama tireloli 73 na haramtacciyar shinkafar waje da kuma sauran haramtattun kayayyakin da darajarsu ta kai N4.8bn a cikin watannin shekarar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kuma kara da cewa, hukumar ta samar da kudaden shiga N58bn daga watan Fabrairun 2022 tun lokacin da gwamnati ta ba da umarnin bude iyakar Idiroko.
Ba gudu ba ja da baya wajen kama shinkafar waje
Bamidele ya ce hukumarsa ba za ta tsorata ba don kawai ana farmakar jami’anta, inda ya roki masu ruwa da tsaki da ‘yan kasa da su ci gaba da ba gwamnati hadin kai wajen hana shigo da haramtattun kayayyaki.
Farar shinkafa ‘yar waje na daya daga cikin kayayyakin da gwamnatin Najeriya ta haramta shigo dasu kasar nan ta iyakar kasa, rahoton Punch.
Hakazalika, tana daga cikin kayayyakin da aka fi shigo dasu Najeriya, inda ake kashe biliyoyin kudade wajen shigo da ita.
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku
Yin fasa-kwabrinta, musamman daga jamhuriyar Benin ya zama babban abin damuwa ga gwamnatin Najeriya na tsawon shekaru.
Kamen da aka yi a kwanakin nan na nuni da cewa, ‘yan fasa-kwabri na kokarin shigo da shinkafa ne a shirin kirsimeti da sabuwar shekara.
Ba iyaka shinkafa 'yar waje gwamnatin Najeriya ta haramta a shigo da ita kasar nan ba, an haramta shigo da kayayyaki da yawa.
Hakazalika, gwamnati ta haramta fitar da wasu kayayyakin da take ganin kasar ka iya samun matsala idan ana fitar dasu, fatun Jakuna na daga cikin irin wadannan kayayyaki.
Asali: Legit.ng