Bincike ya Tono Yadda Sojojin Kasa Suka Zubar da Juna Biyun Mata 10, 000 a Najeriya

Bincike ya Tono Yadda Sojojin Kasa Suka Zubar da Juna Biyun Mata 10, 000 a Najeriya

  • Bincike na musamman da Reuters ta gudanar ya zargi sojojin Najeriya da zubarwa ‘yan mata da juna biyu
  • A ‘yan shekarun nan, ana zargin an zubar da ciki 10, 000 daga matan da suka samu alaka da ‘Yan Boko Haram
  • Sojoji sun ce binciken ba gaskiya ba ne, kungiyoyi kamar North East Advocacy for Peace sun goyi bayansu

Nigeria - Wani bincike na musamman da gidan yada labaran Reuters ya gudanar, ya zargi sojojin kasan Najeriya da zubar da ciki ba tare da bin doka ba.

Rahoton da aka fitar, ya nuna cewa daga shekarar 2013 zuwa yanzu, sojojin kasa sun zubar da juna biyu akalla 10, 000 da mata da ‘yan mata ke dauke da su.

Sojojin su kan zubar da juna biyu da matan da rikicin Boko Haram ya rutsa da su suke dauke da shi. Kafin yanzu babu wanda ya fitar da wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Ina 'Yan Mata Zasu Sa Kansu: NAFDAC Na Kokarin Sa 'Kafar Wando Da Dillalan Man Bilicin

The Cable da ta bibiyi rahoton, tace sojoji su na amfani da yaudara da kuma karfi ne wajen zubar da juna biyun matan da ke tsare a hannun jami’an tsaron.

An yi magana da mutane 33

Kafin fitar da labarin, an tattauna da mata 33 da abin ya faru da su. Reuters tayi hira da ma’aikatan asibiti da soji, sannan tayi nazarin takardu wajen binciken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mafi yawan lokaci, ana zubar da cikin ne ba tare da sanin matan da ke dauke da su ba. Juna-biyun wata biyu zuwa na wata takwas ba ya tsira a wajen sojoji.

Sojojin Kasa
Sojojin Najeriya a Damasak Hoto: www.reuters.com
Asali: UGC

A duk matan da aka yi hira da su, daya ce kurum ta bayyana cewa an nemi izininta kafin a zubar mata da ciki. Sojojin na gudun a haifo wasu ‘yan ta’addan.

Sauran kuwa sai da karfi da yaji ake tursasa masu domin ganin sun rasa abin da suke dauke da shi. Wasu lokutan har da duka da amfani da karfin bindiga.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kassara 'yan ta'adda, sun ragargajiya maboyar 'yan bindigaa dazukan wata jiha

A matan da ke dauke da juna-biyun, har da masu shekaru 12 da haihuwa. Ana zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka yi masu fyade har suka samu karuwa.

Sharri ne - Jami’an tsaro

Jaridar Punch tace hedikwatar tsaron Najeriya ta bakin darektanta na yada labarai, Manjo Janar Jimmy Akpor ta karyata rahoton, tace sam ba gaskiya ba ne.

Janar Jimmy Akpor yace akwai kananan yara 41, 000 a cikin ‘Yan ta’addan Boko Haram 82, 064 da suka sallama kansu, kuma cikinsu ba a hallaka kowa ba.

Kungiyoyi masu zaman kansu irinsu North East Advocacy for Peace sun yi tir da aikin gidan labaran, suka zarge su da kokarin bata sunan sojojin Najeriya.

Shirin zaben 2023

Rahoto ya zo cewa Jakadar kasar Birtaniya ta hadu da Shugaban Jam’iyyar APC a Sakatariyarsu a Abuja, ta ja kunne a kan murde zaben da za ayi a 2023.

Kara karanta wannan

Tsananin yunwa: Bidiyon mata 'yan Arewa na wawar shinkafa a kan tunkuya ya tada hankali

A wajen Catriona Laing da kasar Ingila, babu bambanci tsakanin Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na APC, PDP, LP da NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng