Majalissar Dattijai Tace Wasu Ma'aikatun Gwamnati Kan Iya Rasa Kasafin Kudinsu

Majalissar Dattijai Tace Wasu Ma'aikatun Gwamnati Kan Iya Rasa Kasafin Kudinsu

  • Majalissar Dattijai da majalissar Wakilai na da alhakin kiran manya da 'kananan ma'aikatun gwamnati dan su kare daftarin kasafin kudinsu
  • Majalissar Dattijai na taza da tsifa game da kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya kai gabanta wanda ya kunshi kashe sama tiriliyan N18
  • An samu cushen N206b a kafasin kudin ma'aikatar jinkai da wal-walar jama'a

Abuja: Majalisar dattijai ta yi barazanar cewa ba za ta bawa wasu ma’aikatu da hukumomi (MDAs) sama da 100 kasafin kudin su ba muddin suka gaza bayyana a gaban kwamitin kwamitin majalissar nan da mako guda.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya yi wannan gargadin bayan fitar da sunayen sama da ma'aikatun gwamnati da hukumomi sama da 100 da suka kaucewa umarnin shugaban kwamitin bin diddgin kudin da kasafi.

Kara karanta wannan

An Daure Dan Shugaban Kasa Sabida Laifin Cin Hanci Da Rashawa

Majalissa
Majalissar Dattijai Tace Wasu Ma'aikatun Gwamnati Kan Iya Rasa Kasafin Kudinsu Hoto: The Nation
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Urhoghide ya ja hankalin majalisar dattijai game da ki amincewar hukumomin da abin ya shafa da su bayyana a gaban kwamitinsa don amsa tambayoyin da babban mai binciken kudi na tarayya ya gabatar a kansu tun 2015.

Ya ce duk kokarin da aka yi na ganin jami’an hukumar sun kare tambayoyin ko zargin da ake musu yaci tura. Rahotan jaridar The Nation

A cikin jawabinsa, Lawan ya ce:

“Ya kamata hukumomi su ringa girmama batun da muka mika musu tare da bin umarnin abinda suka gani a rubuce muddin wani daga zauran nan ne ya rubuta musu, ba dole sai mu ba".
“Sabida kasa bayyana a gaban mu, mun basu sabon kwanan wata. kuma inda suka sake sabawa toza mu rike da kasafin su har sai sun zo".

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Indonesiya Ta Amince Da Haramta Jima'i Kafin Aure

"Duk wani jami'in gwamnati dole ne ya kasance a shirye ya bayar da rahoto a gaban majalisar dokokin kasa. Yakamata su kasance a shirye.

Lawan Yace :

“Ya zo a karkashin doka ta (42) da (95) cikin kudin tsarin mulki ya ayyana karara ikon da kwamitin da ke kula kudi da bin didigin aiyuka na majalisar dattijai, umarnin gayyatar ko wacce ma;aikata ko hukuma".

Hukumomi da Ma'aikatun Da Abin Ya Shafa

Hukumomin sun hada da ofishin Akanta Janar na tarayya, ma’aikatar harkokin cikin gida, hukumar sojojin Najeriya, ma’aikatar tsaro, rundunar ‘yan sandan Najeriya,

Sauran sun hada da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, ofishin kasafin kudi na tarayya, ma’aikatar kula da babban birnin tarayya. ma'aikatar Noma, Hukumar Kula da Nukiliya ta Najeriya da Hukumar Kula da hanyoyin ruwa ta Najeriya.

Cikin ma'aikatun harda Ma’aikatar Harkokin Waje, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, Ma’aikatar Wasanni da Ci gaban Matasa, Asusun Tallafawa Manyan Makarantu da Kwalejin Tsaro ta Najeriya, da dai sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel