Malamin Makaranta a Katsina, Laminu Saminu Ya Sheke Abokinsa da Gubar Bera, Ya Sace Motarsa
- Wani mugun aboki ya hallaka abokinsa da gubar bera domin kawai ya saci motarsa a jihar Katsina
- ‘Yan sanda sun yi bincike, an gano inda wannan matashi yake tare da fara yi masa binciken ya fadi gaskiya
- Bayan dogon bincike, ya shaidawa ‘yan sanda yada ya bi ya kashe abokinsa tare da jefa gawarsa a rijiya
Jihar Katsina - Wani malamin makaranta mai shekaru 29, Laminu Sani ya shiga hannun hukuma bisa zargin sheke abokinsa, Sanusi Bawa wani ma’aikacin tsaron ‘Civil Defence’ a jihar Katsina da gubar bera.
An ruwaito cewa, Sanusi aboki ne ga Laminu, wadanda gaba dayansu daliban ajin karshe ne a kwalijin ilimi ta tarayya da ke Katsina, rahoton PM News.
Malamin da ke zaune a unguwar Bakin Kasuwa da ke karamar hukumar Mani ta jihar ya jawo abokin nasa ne zuwa wani kango, inda ya bashi guba ya mutu.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihjar SP Gambo Isa a cikin wata sanarwa, daga nan ne Laminu ya sace motar Sanusi ya yi awon gaba da ita.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayanin yadda lamarin mara dadi ya faru
A cewar sanarwar ‘yan sandan:
“Wanda ake zargin ya jawo wanda ya kashen ne tare ce masa ya ajiye motarsa, suka shiga kango, inda ya bashi damun Fura da Nono da ya saka ma guba.
“Bayan shan Furar, jami’in tsaron ya fita daga hayyacinsa.
“Daga nan ne wanda ake zargin ya muka masa sanda a ka har sai da ya mutu.
“Sai kuma ya dauki gawarsa ya jefa a cikin wata rijiya a cikin wani gida ya tura kasa.”
Hakazalika, hukumar ta ce daga nan ne Laminu ya samu damar yin awon gaba da motar wannan abokin nasa na makaranta, People Gazette ta tattaro.
Yadda aka yi aka kamo Laminu
Kakakin na ‘yan sanda ya kara da cewa:
“A yayin bincike, ‘yan sanda sun gano wanda ake zargin ya kira matar marigayin a waya inda yace mata ta kawo masa takardun motar mijinta.”
Gambo ya kara da cewa, ‘yan sanda sun bi diddigi kana suka kai ga kame wannan mugun aboki, kuma tabbas ya amsa laifin da ya aikata.
Ya kuma bayyana cewa, an gano ledar guban bera, sanda, mota kirar Volkswagen Golf mai lamba AA 266 KUF a hannun wanda ake zargin.
Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da bincike kan lamarin kafin daga bisani a gurfanar dashi a gaban mai kotu.
Wani malamin makaranta kuma amanar malanta da iyaye ya yi ya hallaka dalibarsa a jihar Kano, lamarin ya haifar tashin hankali.
Asali: Legit.ng