Ba a Gama Bikon ASUU Ba, Kishiyarta CONUA Za Ta Maka Buhari a Kotu

Ba a Gama Bikon ASUU Ba, Kishiyarta CONUA Za Ta Maka Buhari a Kotu

  • Yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana da ASUU, sabuwar kungiyar malaman jami’a ta bayyana yiwuwar maka gwamnati a kotu
  • Wannan na zuwa ne bayan da gwamnati ta gaza biyan mambobinta albashin watannin da ASUU ta yi tana yajin aiki
  • Kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta samu kishiya tun bayan da ta gaza samun mafita daga gwamnati, yanzu kishiyar ta kaure da gwamnati

FCT, Abuja – Sabuwar kungiyar malaman jami’a ta CONUA ta bayyana rashin jin dadinta da yadda gwamnatin tarayya, musamman ma’aikatar kwadago kan yadda aka gaza biyan mambobinta albashi.

Kungiyar ta bayyana yiwuwar daukar matakin doka kan gwamnatin Najeriya bisa take hakkinta da kuma rashin kulawa da bukatun mambobinta, Daily Trust ta ruwaito.

Idan baku manta ba, ministan kwadago, Chris Ngige ya ba kungiyar CONUA da NAMDA takardar shaidar rajista a watan Oktoba yayin da yajin aikin ASUU ya kara kamari.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU Na shirin yin Zanga-Zangar Sabida Kin Biyanta Albashi Da Gwamnatin Tarayya Tayi

A lokacin, gwamnati ta amince da sahihancin kungiyoyin biyu ne a kokarinta na yiwa ASUU kishiya kasancewar ta gaza daidaitawa da gwamnati a wani yajin aikin da ta yi.

CONUA na shirin yin fushi da gwamnatin Buhari
Ba a Gama Bikon ASUU Ba, Kishiyarta CONUA Za Ta Maka Buhari a Kotu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban kungiyar CONUA, Dr Niyi Sunmonu ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Talata 6 Disamba, 2022 cewa, duk da gwamnatin ta san mambobinta ba sa cikin dambarwar yajin aikin ASUU, amma ta gaza biyansu albashi na watanni 8 da ma watan Nuwamba.

Gwamnati ta saba doka da ta ki biyan mambobin CONUA albashi

Ya bayyana cewa, rashin biyan mambobin albashinsu na watanni 8 ya saba da tadanin doka, inda yace ya rataya a wuyan gwamnati ta biya ma’aikatanta da babu ruwansu da batun yajin aiki.

Ya bayyana cewa, mambobin kungiyar sun bi doka, inda suka yanke yin abubuwa sabanin tafiyar da ASUU ke yi na yajin aiki da suka dade suna ciki a wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Dan takarar gwamnan APC ya ce zai yi amfani da baiwar 'Yahoo Boys'

A cewar sanarwar, CONUA ta aike da wasika ta musamman ga minista Ngige a watan Afrilu, inda ta bayyana babu ruwanta da yajin aikin da ASUU ke yi, rahoton SaharaReporters.

Hakazalika, ta ce CONUA ta bayyana karara a wani taron ‘yan jarida da ta gudanar a ranar 19 ga watan Agusta cewa, sam kungiyar ba ta cikin yajin ASUU, kuma dokar gwamnati na ‘Babu aiki babu albashi’ bai shafe ta ba.

A cewar sanarwar, kungiyar ta kuma rubuta wasika ga akanta-janar na kasa da ma ministan kwadagon don tuna musu cewa, kuskure ne ayyana cewa, mambobinta suna cikin yajin aikin da ASUU ke ciki.

A wani labarin kuma, ASUU ta ce za ta sake ballewa da yajin aikin da ba a taba gani kan yadda gwamnati ta ki biyan mambobinta cikakken albashin watanni 8.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.