Babu wanda za'a hukunta saboda nadin matattu — Buhari
- Babban hadimin shugaban kasa ya ce babu dalilin da zai sa a hukunta wadanda suka fitar da sunayen matatu daga cikin sabbin nadin da Buhari yayi
- Garba Shehu ya ce an shirya jerin sunayen sabbin nadin da shugaban kasa yayi shekaru biyu da suka gabata
Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce babu dalilin a zai sa a hukunta wadanda suka fitar da sunayen wasu matattu daga cikin sabbin nadin da shugaba Buhari yayi.
A ranar juma’a 29 ga watan Disamba aka fitar da sunayen sabbin nadin mukamai na hukumomin wasu ma’aikatan gwamnati da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.
Amma abun mamaki sai aka ga sunayen wadanda suka mutu a cikin sabin nadin shugaban kasa, wannan al’amari ya janyo cecekuce tsakanin yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.
Sai dai babban hadimin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya ce, an shirya jerin sunayen ne fiye da shekaru biyu da suka gabata, amma sai aka ajiye su domin sukar da wasu gwamnoni suka yi.
KU KARANTA : El-Rufai da Lai Mohammed shahararrun maƙaryata ne - Jam'iyyar PDP
Garba Shehu ya ce bai ga dalilin da zai sa a dauki matakin ladabtarwa akan wadanda suka saki sunayen ba.
Garba Shehu ya ce za a sauya sunayen matattun mutanen da na wasu yan kasar da suka cancanta.
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng