An Kama Hatsabibin Dan Damfara A Bauchi Da Katin ATM 31, Ya Fallasa Yadda Ya Ke Sace Kudin Bayin Allah
- Dubun wani hatsabibin dan damfarar katin ATM a jihar Bauchi mai suna Micheal Joseph ta cika bayan yadade yana cin karensa babu babbaka
- Hakan ya faru ne bayan wata baiwar Allah da Joseph ya so ya damfara ta sanar da jami'an tsaro
- Yayin da jami'an tsaro suka caje shi, sun gano katin ATM 31 daban-daban, daga nan ya amsa cewa shi dan damfara ne
Bauchi - Yan sanda sun kama wani Micheal Joseph da ya kware wurin damfarar mutane masu son cire kudi a na'urar ATM da sunan taimakonsu.
An kama shi ne a layin Bank Road da ke birnin Bauchi kamar yadda PM News ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin yan sandan jihar SP Ahmed Wakil ya ce an samu katin ATM 31 na bankunan daban-daban a jikin wanda ake zargin cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata.
Ya kara da cewa an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin damfarar wata mata a gaban na'urar ATM na banki a Bauchi.
Yadda aka kama Joseph
A lokacin da ta ke layin ATM, wanda ake zargin ya dage yana son ya san irin ATM din da matar za ta cire kudi da shi hakan yasa hankalinta bai kwanta ba ta kai kararsa wurin jami'an tsaro a banki.
Bayan hakan, an kamwa wanda ake zargin aka kuma caje shi aka gano katin ATM daban-daban guda 31, rahoton LIB.
Abin da wanda ake zargin ya fada wa yan sanda
Yan sanda sun ce bayan masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ce ainihinsa na jihar Benue ne, ya taho Jihar Filato yana neman aiki inda ya yi aikin direban bus na shekaru 3.
Kakakin yan sandan ya ce:
"Wanda ake zargin ya ce wani Magaji dan jihar Kano ya koya masa damfarar lokacin da suka hadu a mashayar giya a Jos, Jihar Filato."
Joseph, a cewar yan sandan ya kan tattara katin ATM daban-daban ya tafi wurin na'urar ATM domin neman wadanda ba su iya cire kudi daga na'uarar da kansu ba.
Daga nan sai haddace lambar sirrin wanda ya taimaka kuma ya yi gaggawa ya sauya katinsu ya mika musu wani irin nasu da ke hannunsa.
Yan sanda sun ce bincike ya nuna wanda ake zargin ya damfari mutum na farko N18,000.
Ya kuma sake damfarar wani N25,000 a wani bankin amma asirinsa ya tonu lokacin da ya yi yunkurin damfarar wata mata a Bauchi.
Sanarwar ta kare da cewa:
"Ana cigaba da bincike kuma idan an kammala za a gurfanar da wanda ake zargi a kotu."
An Kama Yan Damfara Da Katin ATM 36, Sun Bayyana Yadda Suke Damfarar Mutane
Yan sanda a jihar Neja sun yi nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi yan damfara ne da sunan taimakon mutane cire kudi a ATM.
The Nation ta rahoto cewa James Amaonye dan shekara 33 da Victor Okebugwu dan shekara 32 sun shafe fiye da shekaru biyu suna wannan mummunan dabi'a ta damfarar ATM.
Asali: Legit.ng