Yan ɗamfarar da aka kama da katin ATM 36 sun bayyana yadda suke yaudarar mutane

Yan ɗamfarar da aka kama da katin ATM 36 sun bayyana yadda suke yaudarar mutane

Jami'an 'yan sanda a jihar Niger sun kama wasu maza biyu, a babban birnin jihar MInna dauke da katin cire kudi a na'urar ATM guda 36.

'Yan sandan sun ce wadanda ake zargin suna damfarar mutane da suka zo cire kudade a naurar ta ATM ne da sunan taimaka musu.

Victor Okebugwu mai shekaru 32 da James Amaonye mai shekaru 33 sun shafe fiye da shekaru biyu suna damfarar ta ATM kamar yadda The Nation ta ruwaito.

An 'yan damfara biyu da katin ATM 36 da layukan waya 24 a Niger
An 'yan damfara biyu da katin ATM 36 da layukan waya 24 a Niger. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Masari ya haramta bara a Katsina, ya yi wa islamiyoyi gargadi

Amaonye ya ce sun fara damfarar ne a babban rukunin kantina da ke Minna, Obasanjo Complex daga nan kuma suka fara zuwa bankuna.

Ya ce, "Idan mun ga mutanen da suke bukatar taimako a gaban na'urar ATM, mu kan matsa kusa da su da sunan taimako. Mafi yawancin lokaci suna bari mu taimaka musu.

"Mu kan sauya katinsu da jabu wasu lokutan kuma mu kan aika kudade daga asusun ajiyar su zuwa namu ba tare da sun sani ba. Mun dade muna wannan harka."

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya tabbatar da kama wadanda ake zargin inda ya ce 'yan sandan sun dade suna lura da su.

Abiodun ya ce katin na ATM 36 na bankuna daban–daban ne, an kuma gano layin waya, sim card, guda 24 a hannun su.

Abiodun ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164