Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Magantu Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na Tinubu Da Shettima

Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Magantu Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na Tinubu Da Shettima

  • Sheikh Ibrahim Daimagoro, malamin addinin musulunci a jihar Osun ya ce ba laifi bane zaben tikitin musulmi da musulmi
  • Daimagoro ya yi wannan jawabin ne wurin wani taro a Osun inda ya ce mutanen jihar sun zabi gwamna da mataimaki kirista don haka ba laifi bane a zabi shugaban kasa da mataimaki musulmi
  • Malamin ya ce abin da ya fi muhimmanci shine al'umma su zabi shugaba wanda ya cancanta kuma zai iya kawo cigaba ba tare da la'akari da addini ba

Osun - Malamin addinin musulunci, Sheikh Ibrahim Daimagoro, ya ce babu wani matsala idan dan takara musulmi ya zabi wani musulmin ya zama abokin takararsa kamar yadda jam'iyyar APC ta yi a tikitin shugaban kasa a zaben 2023, rahoton Blueprint.

Daimagoro, yayin jawabi a taron addu'a da aka yi don gwamnan jihar Kwara, AbdulRahaman AbdulRazaq, a Ilorin a ranar Litinin ya bada misalin zaben jihar Osun inda gwamna da mataimakinsa dukkansu kiristoci ne don haka ba laifi bane idan APC ta tsayar da musulmi da musulmi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Shahararriyar Jihar Najeriya Ya Bayyana Addinin Ya Zamto Mafi Samun Sabbin Mabiya A Jiharsa

Shettima, Kashim
Babban Malamin Addinin Musulunci Ya Magantu Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na Tinubu Da Shettima. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Daimaigoro ya ce mutanen jihar Osun sun yi watsar da batun addini ta hanyar zaben jam'iyyar PDP da ta tsayar da kirista da kirista a matsayin gwamna da mataimaki, rahoton The Punch.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan PDP ta yi tikitin kirista da kirista a Osun, ba laifi bane APC ta yi a matakin shugaban kasa - Sheikh Daimagoro

Malamin addinin musuluncin ya ce:

"Idan ba matsala bane mutanen jihar Osun su zabi tikicin kirista da kirista na PDP, toh ba laifi bane idan yan Najeriya na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima, dukkansu musulmi.
"Abin da ya kamata ya fi muhimmanci a zukatan yan Najeriya shine zaben wanda ya cancanta kuma Tinubu zai iya habbaka Najeriya zuwa mataki na gaba."

Duk da cewa an kira taron ne don bikin zagayowar ranar haihuwar tsohon kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Kwara, Alh AbdulHameed Sambo, an mayar da shi taron addu'a ga Gwamna Abdulrazaq da Asiwaju Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Majalisar Dokokin Indonesiya Ta Amince Da Haramta Jima'i Kafin Aure

Wasu cikin manyan bakin da suka halarci taron

Manyan mutanen da suka halarci taron sun hada da mashawarci gwamnan jihar Kwara kan tsare-tsare, Saadu Salahu; tsohon dan majalisar jihar, Barista Bamidele Aluko; ciyaman din hukumar kula da maniyyatan jihar Kwara, Dr AbdulKadir Sambaki; Jigon APC, Alh Baba Adefalu; Birgediya-Janar Agbabiaka; da tsohon sakataren dindindin, Alhaja Mopelola AbdulRahman da wasunsu.

Manyan Yan APC Da Ba Su Goyon Bayan Tikitin Musulmi Da Musulmi A 2023

Tun dai a watan Yulin shekarar 2022 ne dan takarar shugaban kasa na APC, Ahmed Bola Tinubu ya zabi Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Wannan zabin ya tada kura a jam'iyyar ta APC da matakin kasa musamman daga kiristoci da ke ikirarin an nuna musu wariyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164