Dalibar Jami’a Aji 5 Ta Bata, Hukumomin Tsaro Sun Fara Bincike a Jihar Osun
- Wani yanayi mara dadi ya faru a wata jami’ar Najeriya, inda dalibar aji biyar a fannin jinya ta bata ba a san inda ta shiga ba
- Hukumar jami’a ta fara bincike, inda ta bayyana halin da ake ciki a yanzu da kuma binciken da DSS suke yi
- Ana yawan samun lokuta da dama a Najeriya da dalibai ke fita daga makaranta a neme su a rasa cikin kankanin lokaci
Jihar Osun - Wata dalibar aji biyar a fannin jinya a jami’ar jiha ta Osun da ke Osogbo, Popoola Zainab ta fice daga makaranta, inda ta ajiye wata takarda da har yanzu hukumomi ke ci gaba da bincike a kai.
An ruwaito cewa, an ayyana batan budurwar ce a ranar Lahadi daga hukumomin jami’ar, kuma har ya zuwa yanzu ba a ji labarin inda ta shiga ba, Vanguard ta ruwaito.
Jami’an hulda da jama’a na jami’ar, Ademola Adesoji ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin, inda ya ce tuni aka sanar da ofishin tsaron jami’ar, inda aka fara bincike.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mun shigar da kara kan lamarin. Mun samu bayanai da daren jiya inda aka ce ta fita ne, da kuma samu bayanan, mun sanar da shugaban tsaron jami’ar shi kuwa ya ayyana fara bincike."
Dalibar ta ajiye wata takarda kafin batanta
A bangare guda, ya ce budurwar ta ajiye wani rubutu, inda yace ana bincike kan rubutun, kuma maganar ta je gaban hukumar tsaro ta farin kasa (DSS) domin bincike lamarin a tsanake.
Da aka tambayi Ademola game da rubutun da budurwar ta yi ya ce:
“Ban samu ganin abin da ta rubuta ba. Don haka, ba zan iya yin magana a kai ba.
“Tana zama ne a wajen makaranta. Mun samu labarin batanta ne bayan da ta daina halartar aji ga kuma kawayenta na yada labarinta a yanar gizo.
“Jami’in hulda da dalibai ya yi kokarin tambayar kawayenta wasu tambayoyi kuma ta nan ne muka samu bayanin ta bata.
“Shugaban tsaron jami’ar tare da hadin gwiwar jami’in hulda da dalibai sun fara bincike. Da rahotonsu muka yi amfani wajen ba hukumar ‘yan sanda da DSS.”
Daga karshe, rahoton Punch ya ce an ba da lambar wayar da za a kira idana aka samu labarin wannan daliba kamar haka: 08144033481.
Dalibar BUK ta rasu tana tsaka da sallah
A wani labarin kuma, kun ji yadda wata dalibar jami'ar Bayero a jihar Kano ta kwanta dama yayin da take tsaka da yin sallah.
Binta Isa ta rasu ne a dakin kwanan dalibai a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Rahoto daga jami'ar BUK ya bayyana cewa, dalibai asalinta 'yar jihar Kogi ne, karatu ne ya kawo ta jihar Kano.
Asali: Legit.ng