Masu Garkuwa Da Mutane Sun Yi Awon Gaba Da Wani Kwamishina A Jihar Benue

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Yi Awon Gaba Da Wani Kwamishina A Jihar Benue

  • An shiga halin fargaba a jihar Benue bayan yan bindiga sun yi awon gaba da kwamishinan gidaje da raya birane, Ekpe Ogbu
  • Maharan sun sace Ogbu ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba a hanyar Otukpo-Ado da ke mararrabar Adankar
  • Da take tabbatar da lamarin, gwamnatin jihar ta bayyana cewa ana nan ana kokarin ceto kwamishinan kuma an kwato motar da yake tafiya da shi

Benue - Yan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan gidaje da raya birane na jihar Benue, Ekpe Ogbu.

Channels TV ta rahoto cewa an sace Ogbu a mararrabar Adankari da ke hanyar Otukpo-Ado a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba.

Yan sanda
Masu Garkuwa Da Mutane Sun Yi Awon Gaba Da Wani Kwamishina A Jihar Benue Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Gwamnatin Benue ta tabbatar da lamarin

Punch ta kuma rahoto cewa kwamsihinan ya halarci wani taron coci, inda Sanata Abba Moro, mai wakiltan Benue ta kudu ya mika lamuran kamfen dinsa da ya kaddamar ga Allah, a hanyarsa ta zuwa kauyensa da ke NDEKMA ne abun ya faru.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yan Baranda Sun Sake Kona Ofishin INEC a Wata Jihar Kudu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai ba gwamnan jihar, Samuel Ortom shawara kan harkokin tsaro Kanal Paul Hemba (mai ritaya) ya tabbatar da sace Ogbu.

Hemba wanda ya zanta da manema labarai kan sace kwamishinan ya bayyana cewa rundunar yan sanda a Otukpo ta yi nasarar samo motar Hilux da Ogbu ke tafiya a ciki.

An kuma tattaro cewa maharan basu kira kowa daga dangin kwamishinan ba, amma dai an fara kokarin ganin an kubutar da shi daga hannun miyagun.

Mararrabar Adankari ya zama wuri mai matukar hatsari inda ayyukan sace-sacen mutane ke yawa afkuwa, an yi garkuwa da akalla mutum uku a wannan waje.

A baya, an yi garkuwa da wani limamin katolika, farfesan jami'ar jihar Benue da wani dan siyasa daga Otobi a wannan wajen a lokuta mabanbanta.

Yan sanda sun kama saurayi da budurwa da suka binne dan da suka haifa

Kara karanta wannan

Rikici: Makiyaya da manoma sun yi fada, an kashe mutum 8 har da yada, an kone gidaje 47 a jihar Arewa

A wani labari na daban, yan sanda a jihar Jigawa sun cafke wata mata bayan kama ta da laifin binne jinjirin da ta haifa a cikin bandakin gidansu.

Yan sandan sun kuma kama saurayin da ya yi mata ciki domin dai tare suka kitsa binne yaron dan gaba da fatiha jim kadan bayan haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel