Gwamnoni Sun Karyata Ikirarin Minista Kan Cewa Su Suka Jefa ’Yan Najeriya Cikin Bakin Talauci

Gwamnoni Sun Karyata Ikirarin Minista Kan Cewa Su Suka Jefa ’Yan Najeriya Cikin Bakin Talauci

  • Gamayyar gwamnonin Najeriya sun yi fushi da karamin ministan kudi kan kalamansa na cewa, laifinsu ne karuwar takauci a kasar nan
  • Kungiyar gwamnonin Najeriya ta ce laifin Buhari ne, domin ya gaza kare 'yan kasar da dukiyoyinsu daga 'yan ta'adda
  • Hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana adadin talakawa masu shan fama a kasar nan, lamarin da ya girgiza kasar nan

Najeriya - Gamayyar gwamnonin Najeriya a jihohi 36 sun bayyana kaduwa da shiga mamakin yadda aka kakaba musu laifin jefa kasar nan cikin matsanancin talauci, BBC Hausa ta ruwaito.

Karamin Ministan kasafin kudi, Clem Agba ne ya bayyana wa duniya cewa, gwamnonin Najeriya ne suka jefa kasar cikin matsanancin talauci ba wai shugaba Buhari ba.

Ministan ya fadi hakan ne a wani taron da aka gudanar, inda ya yi tsokaci game da rahoton hukumar da ta fitar da rahoton talauci a kasar nan.

Kara karanta wannan

Satar Kudin Kananan Hukumomi: Gwamnan Kudu Mai Karfin Fada A Ji Ya Gargadi Buhari

Idan baku manta ba, hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar jerin jihohin da suka shiga taskun talauci a kasar nan, inda aka yi jeren daidai da yanayin da jihohin kasar ke ciki.

Gwamnoni sun karyata ministan Buhari, sun ce ba su suka jefa Najeriya a talauci ba
Gwamnoni Sun Karyata Ikirarin Minista Kan Cewa Su Suka Jefa ’Yan Najeriya Cikin Bakin Talauci | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar kididdigar, akalla mutum miliyan 139 ne a kasar ke fama da matsanancin talauci, wanda ke wakiltar kashi sama da 63% cikin 100% na jumillar 'yan kasar.

Ba laifin mu bane, laifin gwamnatin tarayya ne, inji gwamnonin Najeriya

Da suke martani ga kalaman karamin ministan ta bakin kungiyarsu, gwamnonin sun fitar da sanarwar da ke nuna fushinsu da abin da aka jingina musu, wanda a cewarsu ba haka yake ba.

Sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai ta kungiyat gwamnonin Najeriya, Abdulrazaque Bello-Barkindo ta ce bai kamata ministan ya yi irin wadannan kalamai ba.

Hakazalika, kungiyar ta bayyana balo-balo cewa, sam babu alamun gaskiya ko miskala-zarratin a kalamansa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Tona Asirin Gwamnonin Dake Sace Kudin Kananan Hukumomi

Da suke fashin baki ga kamalansa, sun ce maganar wai sun watsar da al'ummar karkara a jihohin ba magana ce mai makama balle tushe ba.

Daga karshe gwamnonin sun ce, laifin gwamnatin tarayya ne a gazawarta wajen kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasar, hakan ya jawo haihawar talauci, TheCable ta ruwaito.

APC ta ce laifin PDP ne jefa 'yan Najeriya a talauci

A wani labarin kuma, jam'iyyar APC mai mulki ta daura alhakin karuwar talauci a Najeriya da yadda jam'iyyar PDP ta gudanar da mulkinta cikin shekaru 16.

Jam'iyyar ta bayyana hakan ne bayan da rahoto ya bayyana karuwa adadin wadanda ke cikin bakin talauci a Najeriya.

A bangare guda, 'yan Najeriya da dama na ganin laifin gwamnatin Buhari da daura 'yan kasar cikin matsanancin talauci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.