An Cafke 'Bokan' Da Ke Kera Wa Yan Bindiga Rigar Kare Harsashi A Katsina

An Cafke 'Bokan' Da Ke Kera Wa Yan Bindiga Rigar Kare Harsashi A Katsina

  • Yan sanda sun kama wani dan shekaru 53 da ake zargin yana kere wa tare da sayarwa yan bindiga rigar kare harsashi
  • Jami'an tsaron sun kuma ce mutumin ya kan yi wa bata gari da yan bindiga addu'o'in sa'a idan za su tafi kai hare-hare
  • Wanda ake zargin, ya amsa laifinsa yayin tambayoyi, ya kuma ce ya kan sayar da kowanne riga kan N60,000

Jihar Katsina - Yan sanda a jihar Katsina sun kama wani mutum dan shekara 53 wanda ake zargin ya kware wurin kera wa yan bindiga da bata-gari rigar kariya daga harsashi tare da yi musu addu'a na samun sa'a.

PM ta rahoto cewa kakakin sandan jihar, Gambo Isah, ya fada wa yan jarida a Katsina a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba cewa wanda ake zargin yana zaune ne a Layin Maiduguri, a karamar hukumar Sabuwa a jihar.

Kara karanta wannan

Wani Jami'in Hukumar Shige Da Fice Ya Rasa Karin Girma Sakamakon Kai Karar Ogansa

Bokan Yan Bindiga
An Cafke 'Bokan' Da Ke Kera Wa Yan Bindiga Rigar Kare Harsashi A Katsina. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

sulke
An Cafke 'Bokan' Da Ke Kera Wa Yan Bindiga Rigar Kare Harsashi A Katsina. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

An kama shi ne a ranar 26 ga watan Nuwamba bayan an tsegunta wa jami'an tsaro abin da ya ke yi, a cewarsa.

Kan nawa 'bokan' ke sayarwa yan bindiga rigar kare harsahin?

Ya kara da cewa wanda ake zargin yana kerewa tare da siyar da rigar kariya daga harsashin kan N60,000 kowanne guda daya ga bata gari da yan bindiga a Katsina, Kaduna da Zamfara.

Isah ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa yayin da ake masa tambayoyi, rahoton The Eagle Online.

Ya ce yan sandan sun gano rigunan kare harsashi na asiri da wasu layyu da guru daga hannun wanda ake zargin.

Kakakin yan sandan ya ce wanda ake zargin ya saba yi wa yan bindigan addu'o'i kada jami'an tsaro su kama su yayin kai hari.

Kara karanta wannan

Ya taro rikici: Direba ya kashe wani mai mota garin tserewa bayan an cika masa tanki a gidan mai a Kaduna

SP Isah ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike.

Dagaci mai aiki tare da yan bindiga ya shiga hannun yan sanda a Katsina

Jami'an yan sandan jihar Katsina sun ce sun kama wani Surajo Madawaki, Dagaci a garin Gobirau da ke karamar hukumar Faskari ta jihar a Katsina kan zargin hada baki da yan fashin daji don halaka wani manomi.

Gambo Isah, mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina ya ce rundunar ta samu kiran neman taimako kan cewa yan fashin daji sun kashe wani Yahaya Danbai a lokacin da ya ke aiki a gonarsa.

Binciken da yan sandan suka yi sun gano cewa dagacin ya hada baki da shugaban yan bindigan ne suka taho suka halaka manomin da ya yi fada da dan bindiga ya halaka shi yayin da ya kawo masa hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel