Bayan Shekaru 7 Ana Bibiyar Mai Garkuwa da Mutane, Dubunsa Ta Cika an Kama Shi
- Bayan shekaru 7 da ayyana ana neman Matthew Nwankwo da tawagarsa kan garkuwa da mutane da suke yi, anyi nasara cafkesa a Anambra
- Tun a baya, Gwamnatin jihar ta rushe gidan Nwankwo a kauyensu na Umuobindi saboda amfani da gidansa da ake yi matsayin maboyar ‘yan bindiga
- An yi caraf da shi tare da mika shi sashen binciken manyan laifuka na ‘yan sandan jihar kamar yadda kakakin ‘yan sanda Ikenga Tochukwu ya bayyana
Anambra - Jami’an ‘yan sanda a jihar Anambra, kudu maso gabashin Najeriya, sun tabbatar da kamen wani da ake zargin shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane wacce aka yi shekaru bakwai da bayyana ana nemansu ido rufe.
Sunansa Matthew Nwankwo, jaridar Premium Times ta rahoto.
An ayyana neman Nwankwo tun shekarar 2015 lokacin da gidansa dake kauyen Umuobindo dake karamar hukumar Oyo ta jihar aka rushe shi bayan gwamnatin jihar ta gane cewa ana amfani dashi matsayin maboyar masu garkuwa da mutane.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar The Nation ta rahoto cewa, ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin a sa’o’in farko na ranar Talata bayan bibiyarsa da suka yi.
Hakazalika, an mika shi sashen bincike na musamman na manyan laifuka.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Toochukwu Ikenga, ya tabbatar da kama wanda ake zargin kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya ya bayyana.
“Wanda ake zargi yana hannun hukuma. Za a sanar muku da duk wani cigaba nan gaba.”
- Mista Ikenga, ‘dan sanda mai mukamin DSP ya sanar.
Garkuwa domin karbar kudin fansa a Najeriya ta zama ruwan dare a biranen kasar nan.
‘Yan siyasa, ‘yan kasuwa da duk wani mai kumbar susa da zai iya biyan kudin fansa har da wadanda ma ba zasu iya biya ba ana kama su.
Anambra tana daga cikin jihohin da garkuwa da mutane tayi katutu a Najeriya. A kalla tsofaffin ‘yan majalisa uku ne aka yi garkuwa dasu a jihar a watanni shida da suka gabata inda aka halaka biyu daga cikinsu.
An sace baki biyar a watan Afirilu a wasu sassan jihar yayin da suke dawowa daga shagalin biki.
Da yawa daga cikin miyagun farmakin da ake kai wa a jihohin yankin suna da alaka da ‘yan awaren Biafra.
Bayan Shekaru 9 Ana Nemansu, Jami’an NDLEA sun kama shahararren mai garkuwa da mutane
A wani labari na daban, jami’an hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA sun yi ram da wani mutum inda ake neman yayansa ido rufe.
An gano cewa sun dade suna harkar miyagun kwayoyi kuma shekaru tara aka kwashe ana nemansu.
Asali: Legit.ng