Aisha Buhari ta Kai Dauki Cikin Rikicin APC a Jihar Adamawa

Aisha Buhari ta Kai Dauki Cikin Rikicin APC a Jihar Adamawa

  • Uwargidan shugaban kasan Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa zata kutsa cikin rikicin jam’iyyar APC da yayi kamari a jihar Adamawa
  • Jam’iyyar ta fada cikin rikici tun bayan da aka yi zaben fidda gwani na Gwamna wanda Aishatu Binani ta lallasa Nuhu Ribadu da tsohon Gwamna Bindow
  • Kotun daukaka kara ta jaddada cewa Sanata Binani ce halastacciyar ‘yar takarar gwamnan jihar, lamarin da ya sake hargitsa jam’iyyar dukkanta

Yola, Adamawa - Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta bayyana shirinta na shiga sasanci a rikicin jam’iyyar APC da yayi kamari a jihar Adamawa.

Aishatu Buhari da Sanata Aishatu Binani
Aisha Buhari ta Kai Dauki Cikin Rikicin APC a Jihar Adamawa. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, rikici ya harke a jam’iyyar APC reshen jihar bayan zaben fidda gwani na jihar wanda Sanata Aishatu Dahiru Binani, ta ci tare da lallasa Malam Nuhu Ribadu wanda yayi watsi da sakamakon tare da garzayawa kotu.

Babbar kotun tarayya dake zama a Yola a watan da ya gabata ta soke zaben fidda gwanin tare da bayyana cewa jam’iyyar bata da ‘dan takarar gwamna a zaben 2023 mai zuwa, lamarin da yasa APC tare da Binani da Ribadu suka garzaya kotun daukaka kara.

Kotun daukaka karar dake zama a Yola, babban birnin jihar Adamawa, a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba ta bayyana Sanata Binani matsayin halastacciyar ‘yar takarar Gwamnan APC a jihar Adamawa a jihar, cigaban da ya sake raba kan jam’iyyar a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, Matar shugaba Buhari a wallafar da tayi a shafinta na Instagram a ranar Talata, tayi magana kan matsayarta kan siyasar Adamawa.

Ta bayyana goyon bayanta cikakke ga shugabannin jam’iyyar tare da mayar da hankali wurin daukar mataki da duba dalilai da hankali a siyasar Adamawa.

Ta kara da yin kira ga shugabanni a arewa da su yi koyi ga tsarin takwarorinsu na Kudu maso yamma ta hanyar sanya mata matsayin mataimaka gwamnan jihohinsu.

Aisha Binani ta lallasa Ribadu da Bindow a zaben fidda gwani

A wani labari na daban, Sanata Aisha Dahiru Binani ta jihar Adamawa ta lallasa Nuhu Ribadu da tsohon Gwamna Bindow a zaben fidda gwanin ‘dan takarar gwamna na APC da aka yi a Adamawa.

Sanata Binani ta zama zakaran gwajin dafi a zaben inda ta samu kuri’un da suka zarta na kowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel