Aisha Buhari: Matashin Da Aka Tura Kurkuku Yana da Jarrabawar Karshe a Jami'a - Lauya

Aisha Buhari: Matashin Da Aka Tura Kurkuku Yana da Jarrabawar Karshe a Jami'a - Lauya

  • Lauyan Aminu Adamu, K Agu yace matashin da yake tsare a kurkuku yana da jarrabawa a gabansa
  • Adamu yana gidan gyaran hali a lokacin da sauran abokan karatunsa suke shirin jarrabawar karshe
  • A dalilin wannan ne Lauya da sauran mutane suke rokon a fito da wannan yaro domin ya karasa digiri

Abuja - K Agu wanda shi ne Lauyan da ya tsayawa Aminu Adamu a kotu, ya bayyana cewa ya nemi 'yan sanda su bada beli saboda uzurin jarrabawa.

Daily Trust ta rahoto K Agu a ranar Laraba, 30 ga watan Nuwamba 2022 yana cewa Aminu Adamu zai fara jarrabawa a ranar 5 ga watan Disamban nan.

Idan matashin ya samu beli, zai iya zana jarrabawarsa ta karshe a jami’ar tarayya ta garin Dutse. Idan bai samu ba, akwai yiwuwar yayi asarar shekara.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Aike Da Dalibin Aminu Gidan Kurkuku Bisa Zargin Cin Zarafin Uwar Gidan Buhari

Lauyan da ya tsayawa dalibin jami’ar ya shaidawa BBC Hausa cewa tun ranar Juma’a ya nemi a bada beli, amma hukuma ba tace masa uffan ba tukuna.

Muna jiran 'yan sanda - Lauya

"Ko a zaman kotun jiya, mun fadawa Alkali mun bukaci ‘yan sanda su ba Aminu beli a kan lokaci, amma ba su ba mu amsar ko za suyi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saboda haka muka bukaci kotu ta ba shi beli saboda larurar rashin lafiya kuma zai fara jarrabawar makaranta a ranar 5 ga watan Disamba.
Aisha Buhari da 'Ya 'yanta
Iyalin Shugaban Kasa Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC
Kuma yanzu kotu ta bada umarni ga ‘yan sanda su gabatar da takardar neman belin da muka shigar saboda ayi aiki a kai, a yau ko gobe.

- K. Agu

Lauya yace tun jiya aka kai shi kotu

Abba Hikima wanda Lauya ne mai kare hakkin mutane ya tabbatar da wannan labarin, yace tun a ranar Talatar nan aka gurfanar da Aminu Adamu.

Kara karanta wannan

Aminu Zai Gurfana Gaban Kotu a Yau Laraba Kan Zargin Cin Mutuncin Aisha Buhari

Lauyan yake cewa abin da mafi yawan mutane ba su sani ba, tun a jiya aka aika matashin gidan gyaran hali duk da jarrabawar jami’a tana gabansa.

Za a batawa yaro rayuwarsa!

Shi kuma Dr. Aliyu Isa Aliyu, wanda malami ne a jami’ar tarayyar da Aminu yake karatu, ya yi magana a shafin Facebook, yace za a lalata rayuwar yaron.

Aliyu Isa Aliyu yace idan matashin bai rubuta jarrabawarsa ba, ba zai samu damar kammala karatun jami’a da wuri ba, an yi asarar karatun tsawon kenan.

Ba rabo da gwani ba...

A wani rahoto, kun ji an yi lokacin da mutanen kasar nan suka rika cin mutuncin Shugaba, Dr. Goodluck Jonathan da uwargidarsa, Patience Jonathan.

Sai ga shi wasu mutane a Twitter suna cewa sun gane kuskurensa wajen sukar Goodluck Jonathan, har suna yi wa tsohon shugaban addu’ar musulunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng