Toroso Ya Zama Kudi, Yadda Dan Najeriya Yake Samar da Wutar Girki da Ta Lantarki Daga Toroso

Toroso Ya Zama Kudi, Yadda Dan Najeriya Yake Samar da Wutar Girki da Ta Lantarki Daga Toroso

  • Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kuka kan tsadar gas din girki, wani dan kasar ya samar da mafita mai saukin gaske
  • Mutumin dan Najeriya ya kirkiri wani nau'in masai da zai ke samar da gas din girki da kuma wutar lantarki ta hanyar amfani da datti
  • Hotunan matashin dan Najeriya a lokacin da yake aikin hada wannan bandaki ya jawo cece-kuce daga 'yan Najeriya

Wani fasihin dan Najeriya ya kera wani nau'in masai mai ban mamaki, wanda zai ke samar da gas din girki da wutar lantarki

Bekwarra Blog, wanda ya yada hotuna da labarin matashin mai daukar hankali a dandalin Facebook mai suna Rant HQ Extention ya bayyana yadda fasahar matashi take da kuma saukinta har ma da irin dadewar da take yi.

Kara karanta wannan

Daga Twitter: Matashi ya jefa kansa a matsala, ya shiga hannu bayan zagin Aisha Buhari

Hotunan yadda matashin ke aikin harhada bandakin da kuma yadda wuta ta fito ya ba jama'a da dama mamaki a shafin sada zumunta.

Matashi ya yi kirkira mai amfani
Toroso Ya Zama Kudi, Yadda Dan Najeriya Yake Samar da Wutar Girki da Ta Lantarki Daga Toroso | Hoto: Bekwarra Blog
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro muku kadan daga abin da jama'a ke cewa game da wannan matashi da zai iya kawo sauyi a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalli hotunan:

Martanin jama'a a facebook.

Iphyie Dickson yace:

"Abin takaici ne yadda 'yan Najeriya suka mayar da hankali ga iskar gas, musamman wadanda suka yi physics da chemistry a makarantunsu.
"Me zai hana ku yi aiki a kan wannan domin sama mana sauki daga wannan tsada.
"Kusan 9500 ake kashewa wajen cika tulun gas mai girman 12.5kg yanzu. Wani lokacin ko wata ma ba zai kai ba. Muna matukar bukatar mafita daga rayuwar kunci ga 'yan Najeriya."

John Aduku yace:

"Hanyar samar da makamashi mai tsafta. Ba sabon abu bane, ku tafi Afrika ta Gabas ku ga yadda ya ba da gudunmawa ga kashi 50% na makamashin da ake amfani dashi a gidaje.

Kara karanta wannan

"Kantin Tafi Da Gidanka": Bidiyon Wani Dan Najeriya Da Ya Mayar Da Baro Babban 'Kanti' Ya Birge Mutane Sosai

"Mazauna karkara a Najeriya ya kamata su rungumi wannan lamari."

Chinenyenwa Chigbu Eno tace:

"Kawata ta makaranta ta taba yin irin wannan, amma na ta na amfani da toroson kaji ne wajen samar da iskar gas."

Magdalene Ishaku Chagwas tace

"Kullum nakn fada babu abu mara amfani a idon injiyan sinadarai, ko da kuwa toroso ne sai ake min dariya. Ina alfahari da wannan mutumin, mu da toroson shanu muke samar da iskar gas din girki."

Mavis Marvelous Mavis yace:

"Kenan yanzu irin wannan, idan baka totsa toroso ba, babu girki kenan."

A wani bangare guda a Arewacin Najeriya, Malam Usman Hadi ya kirkiri hanyar samar da wutar girki ta amfani da ruwan sha da kuma gishiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.