Rahoto: ISWAP ta tabbatar da mutuwar Shekau, ta ce Shekau dan rashawa ne

Rahoto: ISWAP ta tabbatar da mutuwar Shekau, ta ce Shekau dan rashawa ne

- Rahoto ya bayyana dalilin da yasa kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta kashe dan ta'adda Shekau

- Rahoton ya ce, Shekau ya kasance mara imani kuma shugaba dan rashawa, wannan yasa aka kashe shi

- Hakazalika ISWAP din ta bukaci 'yan ta'addan 'yan uwanta da su gujewa fada da aikata ta'addanci

Kungiyar ISWAP mai ikirarin kafa daular Islama, wacce ta balle daga kungiyar Boko Haram, ta tabbatar da mutuwar Abubakar Shekau, tsohon shugaban kungiyar Boko Haram.

Wani rahoton sirri na ‘yan sanda da aka ba TheCable ya ambato wasu manyan kwamandojin ISWAP suna cewa Shekau ya tarwatsa kansa da kansa a ranar 19 ga Mayu bayan arangama da 'yan ta'addan ISWAP.

An ce shugaban na Boko Haram ya kashe kansa ne da bam "lokacin da ya lura cewa mayakan ISWAP na son kama shi da ransa".

KU KARANTA: Ku kirkiri taku kafar: APC ta kalubalanci matasan Najeriya bayan hana Twitter

Rahoto: ISWAP ta bayyana dalilin da yasa ta hallaka shugaban Boko Haram, Shekau
Rahoto: ISWAP ta bayyana dalilin da yasa ta hallaka shugaban Boko Haram, Shekau Hoto: humangle.ng
Asali: UGC

A wani sako, Abu Musab Albarnawi, shugaban ISWAP, ya tabbatar da mutuwar Shekau.

Albarnawi ya bayyana Shekau a matsayin "bijirarren shugaba kuma dan rashawa", yana mai cewa mayakansa sun yi farin ciki da labarin mutuwarsa.

Shugaban ISWAP din ya ce Shekau ya aikata "ta'addancin da ya zarce tunani", ya kara da cewa ya hallaka ne "ta hanya mafi wulakanci". Hakazalika ya ce Shekau ya gwammace ya "wulakanta" a lahira fiye da a duniya.

Albarnawi ya bukaci mayakan ISWAP da ke yankin Tafkin Chadi da kada su zauna su na kallo kawai wani bangare na Boko Haram, wanda har yanzu ke biyayya ga Shekau, ya mamaye gidajensu, yana kashesu tare da sace matansu da ’ya’yansu, ana mai da su bayi.

Ya bukaci kungiyar ta ta'addanci da su zabi tattaunawa a kan fada; idan ba haka ba, karshen su zai zo ba da dadewa ba idan suka zabi yaki tare da aikata ta'addanci., HumAngle ta ruwaito.

"Shin ba ku ga abin da ya faru da shugabanku ba wanda ya fi ku karfi, ya fi ku kwarewa, amma duk da haka an ci galaba akanshi?"

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya shiga matukar jimamin mutuwar TB Joshua

A wani labarin, Wani dan Najeriya da ke zaune a kasar waje ya yi ikirarin cewa wani mutumin kirki ya bayar da gudummawar tankar yaki don yaki da rashin tsaro a kasar.

A wani bidiyo da @lindaikejiblogofficial ta wallafa a shafin Instagram, mutumin da ba a san ko wanene ba ya ce zai kawo tankokin yakin ne zuwa Najeriya inda zai yi amfani dasu wajen yakar mayakan Boko Haram, 'yan bindiga, IPOB da ESN.

A cewarsa, tankar yakin din zata iso Najeriya nan da mako hudu. Ya ce zai tantance ta a tashar jirgin ruwa ta Tin Can a yankin Apapa da ke Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.