Za a Gurfanar Da Aminu Gaban Kuliya a Yau Kan Zargin Cin Mutumin Aisha Buhari – In ji Iyayen Dalibin
- Aminu Adamu Mohammed zai gurfana a gaban wata kotun Abuja a yau Laraba, 30 ga watan Nuwamba
- Za a dai gurfanar da dalibin na jami'ar tarayya da ke Dutse, jihar Jigawa kan zargin cin zarafin uwargidar shugaban kasar Najeriya
- Ana zargin Aisha Buhari da sa jami'an tsaro su kama yaron tare da tsare shi tsawon kwanaki 13
Abuja - A yau Laraba, 30 ga watan Nuwamba ne aka sa ran za a gurfanar da dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Aminu Adamu Mohammed wanda ya caccaki uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, BBC Hausa ta rahoto.
An dai yi zargin cewa jami’an tsaro sun kama matashi Aminu tare da tsare shi tsawon kwanaki 13 ba tare da gurfanar da shi don ya fuskaci shari’a ba.
Jami'anj Tsaro Sun ki Su Bayyana Ko A Wanne Hali Aminu Yake Ciki Baya Da Ya Shafe Mako Guda A Hannunsu
A yanzu haka dai babu tabbaci kan tuhume-tuhumen da hukumomi za su yi wa matashin wanda jami’ai suka dauke ba tare da sanin hukumomin makarantarsa ba bisa umurnin Aisha Buhari.
Batun gurfanar da Aminu na zuwa ne a daidai lokacin da talakawa da wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam da wasu manyan masu fada aji ke kiraye-kiraye tare da neman a sake shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Muna fatan ganin dawowar Aminu don ya zana jarrabawarsa ta karshe a jami'a, Iyayensa
Kanin mahaifin Aminu mai suna Baba Azare ya ce bayan garkame dan nasu na tsawon kwanaki 13, hukumomin sun sanar da su cewa a yau za a gurfanar da shi.
Baba Azare ya ce kamar yadda aka shaida masu, za a gurfanar da shi ne a gaban wata kotu da ke babban birnin tarayya Abuja, sashin Hausa na BBC ta rahoto.
Ya kuma bayyana cewa suna fatan ganin an sake shi domin ya je ya fuskanci jarrabawarsa ta kammala jami'a da za a fara a makarantarsu.
Naja'atu Mohammed ta yi kira ga hukunta Aisha Buhari kan jibgar Aminu
A wani labarin, wata kwamishina a hukumar kula da harkokin yan sandan Najeriya, Naja'atu Mohammed ta bukaci a hukunta uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha bisa zargin dukan Aminu da aka ce ta yi.
Naja'atu wacce ta yi tir da batun daukar doka a hannu da uwargidar shugaban kasar tayi, ta nemi jami'an tsaro su kwamushe ta sannan a hukunta ta.
Asali: Legit.ng