Kungiyar Dalibai Ta NANS Ta Nemi Afuwar Aisha Buhari Kan Kama Aminu Mohammed

Kungiyar Dalibai Ta NANS Ta Nemi Afuwar Aisha Buhari Kan Kama Aminu Mohammed

  • Uwar gidan shugaban kasa ta ci gaba da yin shuru game da kama Aminu Muahmmad, dalibin aji biyar a jami'ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa
  • A baya Aminu ya tafi shafinsa na Twitter, inda ya yi kalaman gatsali ga uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari
  • A wata doguwar wasika, kungiyar daliban Najeriya sun bayyana nemawa Aminu afuwa daga wajen uwar gidan shugaban kasa

FCT, Abuja - Biyo bayan kame Aminu Muhammad, wani dalibin aji biyar a jami'ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa bisa zargin ya zagi Aisha Buhari, kungiyar dalibai ta nemi afuwar uwar gidan shugaban kasa.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, kungiyar ta dalibai ta fitar da sanarwa a rana Talata 29 ga watan Nuwamba ta hannun shugabanta, Usman Barambu, inda suka nemi a sake Aminu.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Ce Wanda Ta Bada Umarni a Cafke Aminu Adamu Inji Kawun Matashi

A cikin sanarwar, NANS ta bayyana kama Aminu a matsayin kamu ba bisa ka'ida ba tare da cewa, har yanzu ba a san inda yake ba har sai da aka gano an kama shi an zarce dashi ofishin 'yan sanda da ke Wuse Zone 2 a Abuja.

NANS ta nemi afuwar Aisha Buhari
Kungiyar Dalibai Ta NANS Ta Nemi Afuwar Aisha Buhari Kan Kama Aminu Mohammed | Hoto: @aishambuhari
Asali: Instagram

Kungiyar ta ce, abin da Aminu bai da bambanci da abin da sauran fusatattun 'yan Najeriya ke yi a kafafen sada zumunta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

NANS ta ce, na sa da ya yi muni ta wata hanyar, kuma na sa ne aka gani har aka kai ga kama shi.

Kamar yadda ya zo a sanarwar, shugaban NANS ya zargi cewa, an ci zarafin Aminu a gidan gwamnati, inda aka ce 'yan sanda sun yi masa dukan tsiya.

NANS ta nemi afuwar Aisha Buhari

Duk da bayyana kokensa, shugaban NANS ya nemi afuwar Aisha Buhari a madadin Aminu, inda yace ya kamata shugabanni da masu rike da mukamai suke jure maganganun suka irin wannan.

Kara karanta wannan

Buhari: Abin da Nake So a Rika Tunawa da Ni Bayan Na Bar Mulki a Kasashen Afrika

Hakazalika, NANS ta bukaci hukumar 'yan sanda da ta ba da bahasin yin garkuwa da Aminu a madadin kama shi yadda doka ta tanada da sanin kowa kuma a rubuce, Punch a ruwaito.

Da yake bayyana irin raunukan da Aminu ya samu, shugaban NANS ya ce:

"Muna kira ga 'yan sanda bisa bukatar jama'a kuma cikin gaggawa su saki Muhammad ba tare da bata lokaci ba ko kuma su fuskanci fushin daliban Najeriya."

A tun farko majiya ta bayyana yadda aka kama Amin tare da tsare shi a wani wuri bayan yi masa dukan tsiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel