Shehu Sani Ya Tona Asirin Abinda Yasa Ake Kai Hari da Kona Ofisoshin INEC

Shehu Sani Ya Tona Asirin Abinda Yasa Ake Kai Hari da Kona Ofisoshin INEC

  • Shehu Sani, tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya yace masu kaiwa Ofisoshin INEC hari makiyan ci gaban ƙasa ne
  • Sanatan ya yi ikirarin cewa maharan dake aikata wannan ɗanyen aikin suna yi ne da nufin hana gudanar da zaben 2023
  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar da cewa wasu miyagu sun ƙona Ofishinta a Izzi, jihar Ebonyi ranar Lahadi

Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya ya fallasa dalilin da yasa 'yan ta'adda da masu aikata manyan laifuka ke kai hari tare da ƙona ofisohin hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC).

Sanata Shehu Sani yace yan ta'adda na aikata wannan ɗanyen aiki ne domin zagon ƙasa da maida hannun agogo baya a shirin INEC na gudanar da babban zaɓen 2023.

Sanata Shehu Sani.
Shehu Sani Ya Tona Asirin Abinda Yasa Ake Kai Hari da Kona Ofisoshin INEC Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Sanatan, wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan Kaduna a inuwar jam'iyyar PDP amma ya sha kaye, ya faɗi haka ne a shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: An Gano Wasu Fitattun Mutane 100 Masu Hatsari Dake Daukar Nauyin 'Yan Ta'adda a Najeriya

'Yan bindiga sun ƙara matsa ƙaimi wurin kai hare tare da ƙone gine-gine da kayayyakin zaɓe a Ofishin INEC a sassan ƙasar nan musamman shiyyar kudu maso gabas.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa ko a jiya, INEC ta sanar da cewa wasu miyagu sun ƙone Ofishinta dake ƙaramar hukumar Izzi a jihar Ebonyi.

Wasu daga cikin kayayyakin da suka ƙone kurmus a harin sun haɗa da Akwatunan jefa kuri'a 340, Injina 14, Teburan dangwala kuri'a 130, Babban Tankin Aje ruwa da adadi mai yawa na Katunan zaɓe.

Meyasa ake kaiwa Ofisoshin INEC hari?

Da yake martani kan lamarin, Shehu Sani, a shafinsa na Tuwita yace maharan maƙiya ne ga cigaban ƙasar nan, waɗanda ba su fatan zabe ya gudana a 2023.

Yace:

"Babbar manufar masu kai hari da ƙone Ofisoshin INEC shi ne zagon ƙasa ga zaɓen 2023, makiyan demokuradiyya ne."

Kara karanta wannan

'Ba Tausayi' Kotu Ta Yanke Wa Mutumin da Aka Kama da Katin Zabe Sama da 100 Hukunci a Sokoto

"Ya rataya a wuyan mutane su kauracewa ta da yamutsi kuma su tashi tsaye kan waɗannan mutanen."

Kotu Ta Daure Mutumin da Aka Kama da Katin Sabe 101 Shekara 1 a Gidan Yari

A wani labarin kuma INEC tace Kotun Majistire a Sakkwato Ta Tura wanda aka Kama da Katin Zaɓe 101 zaman gidan Yari na shekara ɗaya

Kwamishinan tattara bayanai na INEC ta ƙasa, Festus Okoye, a wata sanarwa da ya fitar yace hukumar na ci gaba da bibiyan hukuncin da za'a yanke wa wanda aka kama a Kano.

Yace hukumar zaɓe ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da an hukunta duk wanda ya shiga hannu da makamancin irin wannan laifi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel