NARD: Likitoci 4, 000 Za Su Bar Aiki a Najeriya, Su Koma Asibitocin Kasashen Waje

NARD: Likitoci 4, 000 Za Su Bar Aiki a Najeriya, Su Koma Asibitocin Kasashen Waje

  • Kungiyar NARD ta koka a kan yadda kwararrun Likitoci suke barin Najeriya zuwa kasashen waje
  • Dr. Emeka Innocent Orji yake cewa likitoci 4000 sun shirya tafiya asibitocin ketare saboda neman kudi
  • Orji yace rashin albashi mai tsoka ya jawo aka yi asarar likitoci sama da 2000 a cikin shekaru biyu

Abuja – Kungiyar NARD ta kwararrun Likitoci a Najeriya ta ankarar da jama’a cewa likitoci bila-adadin na ajiye ayyukansu, su koma kasashen waje.

Vanguard ta rahoto kungiyar ta NARD tana cewa likitoci fiye da 4, 000 za su tafi ci-rani a asibitocin kasashen ketare saboda neman kudi mai tsoka.

Kungiyar ta nuna damwarta a kan yadda gwamnatin Najeriya ta ke kin kula da kwararrun likitoci ta fuskar albashi, kula da jin dadi da walwalarsu.

Kamar yadda Dr. Emeka Innocent Orji yake fada, ‘ya ‘yansu 4000 suka nuna suna sha’awar su ajiye aikinsu, su nemi wasu ayyukan a kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: ASUU za ta sake komawa yaji aiki saboda wasu dalilai

An rasa likitoci 2000 a shekaru 2

Duk da tulin adadin masu niyyar barin Najeriya, NARD tace an rasa likitoci 2000 a shekaru biyu da suka wuce alhali za a iya magance wannan matsalar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dr. Emeka Orji wanda jagora ne a kungiyar NARD ta kasar nan tayi kira ga gwamnati tayi abin da ya dace wajen hana a cigaba da asarar malaman lafiya.

Likitoci
Wasu likitoci a asibiti Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

An rahoto likitan yana cewa akwai dalilai da yawa da ke jawo ‘yan kwadago su bar wurin aikinsu, don haka ya kamata a duba dalilan da ke jawo hakan.

Me yake jawo wannan matsala?

Tun daga wahalar aiki, walwala da jin dadin likitoci, albashi da sauran abubuwa, kungiyar kwararrun likitocin tana so a duba koken malaman lafiya.

“A shekaru biyu da suka wuce ko makamancin haka, mun rasa likitoci 2000 ga kasashen Duniya, muna rasa likitoci 100 zuwa 160 duk wata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya Za tayi Karin Albashi, An Bayyana Ma’aikatan da Abin Zai Shafa

Ba kananan ma’aikata muke magana a nan ba, muna maganar manyan kwararrun likitocin da ke barin kasar nan ne, kuma idan kayi bincike a kan abin da ya sa suke tafiya, 80% za su ce karancin albashi ne."

- Dr. Emeka Innocent Orji

Tun 2009 rabon da a duba albashin ma’aikata, babban likitan yake cewa yanzu idan aka yi nazari da Dala, za a fahimci albashinsa raguwa yake yi a yau.

Tinubu zai bar Najeriya

An samu labari Asiwaju Bola Ahmed Tinubu mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC zai tallatawa shugabannin Duniya takarar da yake yi.

Wata sanarwa a shafin kwamitin kamfe na All Progressives Congress tace Bola Tinubu zai shafe kwana da kwanaki tsakanin Amurka da Landan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng