Gwamnatin Katsina Ta Shirya taron Addu'ar Neman Dawowar Zaman Lafiya a Najeriya

Gwamnatin Katsina Ta Shirya taron Addu'ar Neman Dawowar Zaman Lafiya a Najeriya

  • Gwamnatin jihar Katsina karƙashin gwamna Aminu Masari ta gudanar da Addu'ar neman zaman lafiya a Najeriya
  • Bayan kammala addu'o'in, Masari yace Katsina jihar Addini ce kuma a kowane lamari tana fifita Addu'a
  • Manyan kusoshin gwamnatin Katsina, Malamai da Sarakuna sun halarci taron a Masallacin Usman Ɗanfodiyo ranar Litinin

Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta shirya tare da gudanar da Addu'a ta musamman domin rokon Allah (SWT) ya dawo da zaman lafiya a faɗin Najeriya.

A wurin taron Malamai sun ja hankalin mutane su koma ga Allah kana su roki ya dawo da aminci a jihar da ma ƙasa baki ɗaya, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Taron Addu'a a Katsina.
Gwamnatin Katsina Ta Shirya taron Addu'ar Neman Dawowar Zaman Lafiya a Najeriya Hoto: Katsinapost
Asali: Facebook

Da yake hira da manema labarai bayan kammala Addu'o'in a Masallacin Sheikh Usman Ɗanfodiyo, Gwamna Aminu Bello Masari, ya ayyana Katsina a matsayin jiha mai Addini kuma ta yi imani da Addu'a a kan komai.

Kara karanta wannan

Matasan Jihar Buhari Sun Yi Fatali da APC, Sun Yi Alkawarin Tarawa Wani Ɗan Takarar Shugaban Kasa Kuri'u 6m

"Mun zo mu yi Addu'a da nufin Allah SWT ya saukaka mana kuma ya bamu nasara. Mun yi Addu'ar dawowar zaman lafiya a Katsina kuma ga dukkan alamu muna fatan zuwa karshen shekarar nan komai zai wuce."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ayyukan 'yan fashin daji, ta'addanci, fyaɗe, garkuwa da mutane da sauran laifukan da suka hana Katsina ci gaba da ikon Allah muna fatan ganin ƙarshensu zuwa karshen 2022."

- Gwamna Masari.

Menene asalin makasudin shirya taron Addu'o'in?

A nasa jawabin, Alhaji Ibrahim Ahmed, babban mashawarcin gwamna kan harkonin tsaro da ya jagoranci shirya taron Addu'o'in a Katsina, yace:

"Dalilin gudanar da Addu'in shi ne don kara danƙon zumunci da haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin al'ummar Musulmi, haka ne kaɗai zai bamu damar aiki tare da fuskantar burinkanmu a dunkule."

A cewarsa, masana harkokin tsaro sun ce zaman lafiyar da aka samu kwanan nan a Katsina addu'o'in baya ne Allah ya karɓa.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Jingine Siyasa, Ya Bayyana Mutumin Da Ya Cancanci Zama Shugaban Kasa a 2023

"Addu'a ce ta kawo mu halin da muke a yanzu, mun samu ƙarin zaman lafiya kuma mun gode Allah, zamu cigaba da Addu'a. Haka nan zamu cigaba da kokarin haɗa kan junanmu don cimma nasara."

MURIC Ta Fada Wa Musulmi Su Ƙauracewa Wasu Jami'o'in Kirista Saboda Hana Amfani Da Hijabi Da Wasu Dalilai

A wani labarin kuma Ƙungiyar dake fafutukar kare hakkin Musulmai a Najeriya ta shawarci su kauracewa jami'o'in kuɗi mallakin kiristoci.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana cewa ya karɓi korafe-korafe da yawa kan hana Musulmai mata sanya Hijabi a makarantun kuna ana tilasta musu zuwa tarukan Kiristoci.

Akintola ya ƙara da cewa akwar abubuwan tsangwama da dama ya samu labarin ana wa Musulmai a irin waɗannan makarantu, ya nemi iyaye su rika bincike sosai kafin 'ya'yansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel