‘Yan Daba Sun Bankawa Ofishin INEC Wuta, Gobara Ta aka kunne Muhimman Kayayyaki
- ’Yan ta’addan da har yanzu ba a san ko su waye ba, sun kone ofishin hukumar zabe mai zaman kanta dake Ozzi a jihar Ebonyi
- Miyagun sun kone katikan zabe da har yanzu ba a san yawansu ba, janaretoci 14, akwatunan zabe 340, rumfunan zabe 130 da tankunan ajiyar ruwa
- Wannan ne karo na uku da ake kone ofisoshin hukumar zaben a cikin makonni uku kacal, lamarin da ‘yan sanda ke bincika a halin yanzu
Ebonyi - Wasu Mutane da har yanzu ba a gano ko su waye ba sun kone ofishin hukumar zabe mai zaman kanta dake karamar hukumar Ozzi ta jihar Ebonyi a ranar Lahadi, jaridar Punch ta rahoto.
Hakazalika TVC ta rahoto cewa, wannan na kunshe ne a takardar da kwamishin kuma shugaban kwamitin yada labarai da ilimin masu kadai kuri’a, Festus Okoye, ya fitar a ranar Lahadi.
Wannan ne karo na uku da ake kone ofishin INEC a cikin makonni uku bayan farmakin da aka kai jihohin Osun da Ondo.
Lamarin ya faru wurin kafre 10 na safe kuma hakan ya bar babban ginin da wasu kayayyaki da ba a fitar ba a kone.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kamar yadda takardar tace, kayayyakin da suka kone sun hada da akwatinan zabe 340, rumfunan zabe 130, janaretoci 14, tankunan adana ruwa, tebura da kujeru na ofisoshi da kuma katinan zaben da ba a tantance yawansu ba.
Sai dai, hukumar tace jami’an’yan sanda sun fara bincike cikakke kan faruwar lamarin.
Takardar tace:
“Kwamishinan zabe na jihar Ebonyi, Mrs Onyeka Ugochi, ta bada rahoton kona ofishin INEC na karamar hukumar Izzi Iboko ta jihar da safiyan nan.
“Lamarin ya faru ne wurin karfe 10:00 na safe yayin da wasu da ba a sani ba suka bankawa ofishin wuta.
“Duk da babu wanda ya rasa ransa sakamakon farmakin, babban ginin da kayan da ba a iya matsarwa sun kone. “
Takardar ta kara da cewa:
“Wannan ya hada da akwatunan zabe 340, rumfunan zabe 130, janaretoci 14, manyan tankunan ajiyar ruwa, tebura da kujerun ofis na alfarma da katikan zaben da har yanzu ba a san yawansu ba.
“An janyo hankulan ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da su hanzarta fara bincike.
“Abun takaicin shi ne, wannan ne karo na uku da aka kai irin wannan farmakin a cikin makonni uku a jihohohin Ogun da Osun.”
‘Yan ta’adda sun kone ofishin INEC
A wani labari na daban, wasu tsageru da ba a san ko su waye ba sun kone ofishin INEC a jihar Enugu ana tsaka da shirin zabe.
A ranar Lahadin an gano cewa, jami’an hukumar kwana-kwana sun hanzarta zuwa inda gobarar suke don kashewa.
Asali: Legit.ng