Gwamnan Osun Ya Nada Shugaban Ma’aikata, Sakataren Gwamnati da Kakakinsa

Gwamnan Osun Ya Nada Shugaban Ma’aikata, Sakataren Gwamnati da Kakakinsa

  • Sabon gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a gwamnatinsa
  • Nadin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba
  • Ya nada sakataren gwamnati, mai magana da yawun gwamna da kuma shugaban ma’aikatansa, inda nadin ya fara aiki nan take

Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya yi sabbin nade-nade guda uku masu muhimmanci awanni bayan rantsar da shi a kan kujararsa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannunsa a ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba, jaridar The Nation ta rahoto.

Gwamnan Osun yayin bikin rantsar da shi
Gwamnan Osun Ya Nada Shugaban Ma’aikata, Sakataren Gwamnati da Kakakinsa Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Gwamna Adeleke ya nada Alhaji Kassim Akinleye a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar yayin da ya nada Alhaji Teslim Igbalaye mukamin sakataren gwamnatin jihar Osun.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Jingine Siyasa, Ya Bayyana Mutumin Da Ya Cancanci Zama Shugaban Kasa a 2023

Hakazalika, Mallam Rasheed Olawale shine a matsayin mai magana da yawun gwamnan kuma nadin nasu ya fara aiki ne nan take, rahoton The Sun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta ce:

“Na amince da nadin Alhaji Kassim Akinleye a matsayin shugaban ma’aikatan gwamna, Alhaji Teslim Igbalaye a matsayin sakataren gwamnatin jihar sannan Mallam Rasheed Olawale a matsayin kakakin gwamnan.
“Nadin ya fara aiki a nan take.”

Sanata Ademola Adeleke ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan Osun

Mun kawo a baya cewa a yau Lahadi, 27 ga watan Nuwamba ne Sanata Ademola Adeleke ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan jihar Osun.

Yayin bikin, rundunar yan sandan jihar Osun ta zuba jami'an tsaro sosai a filin wasa na garin Osogbo don tabbatar da ganin an rantsar da Adeleke a matsayin gwamnan jihar Osun na shida cikin kwanciyar hankali da lumana.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma: Kalaman Soyayyar Da Matar Osinbajo Tayi Masa a Cikarsu Shekaru 33 da Aure

Sabon gwamnan wanda ya kasance dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya karbi mulki ne daga tsohon gwamna Gboyega Oyetola wanda ya kasance dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a kasar.

A wani labari na daban, mun ji cewa dubban al'ummasun taru a garin Yola domin yiwa yar takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Adamawa, Sanata Aisha Binani maraba da dawowa mahaifarta bayan nasarar da tayi a kotun koli.

A ranar Alhamis da ya gabata ne kotun ya tabbatar da ita a matsayin wacce ta lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar mai mulki wanda aka yi a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng