Sanata Adeleke Ya Tabbatar Gwamnan Osun na 6, Ya Karba Rantsuwa

Sanata Adeleke Ya Tabbatar Gwamnan Osun na 6, Ya Karba Rantsuwa

  • Sanata Ademola Adeleke ya tabbatar sabon zababban Gwamnan jihar Osun na shida bayan rantsuwar da yayi a ranar Lahadi
  • Daidai karfe 11:54 na safiyar Lahadi zababben Gwamnan jihar Osun ya karba rantsuwar ofishinsa daga shugaban alkalan kotun gargajiya na jihar
  • A gaban gagarumin taron jama’a da suka hada da mambobin jam’iyyar PDP, ‘yan uwansa da abokan arziki ya karba rantsuwar

Osun - An rantsar da Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke matsayin gwamna na shida na jihar Osun a safiyar Lahadi.

Sanata Adeleke
Sanata Adeleke Ya Tabbatar Gwamnan Osun na 6, Ya Karba Rantsuwa. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, daidai karfe 11:54 na safiyar Lahadi ne Adeleke ya zama Gwamnan jihar Osun bayan ya karba rantsuwar ofishin gwamnan karkashin jagorancin babban alkalin kotun gargajiya na jihar.

Taron jama’a masu yawa wadanda suka hada da ‘yan jam’iyyar PDP, magoya bayansa da baki daga sassa daban-daban na kasar nan sun shaida hakan.

Karin bayani na nan tafe…

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Asali: Legit.ng

Online view pixel