An Kona Gidan Jigon PDP Awa 24 Bayan Gwamna Ya Masa Kyautar Sabuwar Mota A Babban Jihar Arewa

An Kona Gidan Jigon PDP Awa 24 Bayan Gwamna Ya Masa Kyautar Sabuwar Mota A Babban Jihar Arewa

  • Wasu da ake zargin yan daba ne masu yi wa yan siyasa aiki sun kona gidan jigon PDP a Benue, Mr Akaa Lim
  • Hakan ya faru ne kimanin awa 24 bayan gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya bashi kyautar sabuwar mota
  • Lim, wanda ya yi takarar kujerar majalisa na yankin Buruku ya ce yana zargin abokan hamayyarsa na siyasa ne suka tura a kona gidansa

Jihar Benue - Wasu da aka zargin yan daban ne sun kona gidan jigon jam'iyyar PDP a jihar Benue, Akaa Lim, awa 24 bayan ya karbi kyautan mota daga gwamnan jihar, Mr Samuel Ortom, Daily Trust ta rahoto.

Lim, wanda magoyin bayan gwamnan Benue ne yana Makurdi awanni bayan ya samu kyautar sabuwar mota kirar Sharon lokacin da labarin ya fito cewa an kona gidansa a Gboko East da ke karamar hukumar Gboko na jihar.

Taswirar Benue
An Kona Gidan Jigon PDP Awa 24 Bayan Gwamna Ya Masa Kyautar Sabuwar Mota A Babban Jihar Benue. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru a ranar Alhamis kuma ba a rasa rai ba illa asarar dukiya.

LIB ta rahoto cewa shaidun sun yi ikirarin cewa wutan, wanda ya lalata wani sashi na gidan ba matsalar lantarki bane domin ba a ja wuta a sashin ba.

Sun yi ikirarin cewa akwai yiwuwa masu adawa da Lim a siyasa suna da hannu a lamarin domin ya yi takarar kujerar majalisar jihar na mazabar Buruku a zaben fidda gwani amma ya sha kaye.

Wani shaidan da ya nemi a boye sunansa ya ce:

"Wasu na fushi da shi saboda yana tare da Ortom. Sun yi tsammanin ya raba jiha da shi sakamakon rikicin da ake tsakaninsa da wasu yan jam'iyyar."

Amma, Lim ya shaida wa yan jarida cewa ya gode wa Allah tunda ba a rasa rai ba sakamakon gobarar, ya kara da cewa yana zargin abokan hamayarsa ne suka kona gidansa.

Lim ya ce a yanzu ba zai iya nuna yatsa ya ce ga wadanda suka yi abin ba, ya kara da cewa wadanda suka yi barnar sun lalata kayan miliyoyin naira kafin su kona gidan.

Martanin yan sandan jihar Benue

Mai magana da yawun yan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, ta ce bata riga ta samu bayani kan afkuwar lamarin ba.

Wasu mahara sun cinnawa gidaje 10 wuta a wata unguwa a Kano

Wasu mahara da ba a san ko su wanene ba sun kai hari unuwar Dan Jamfari a kauyen Barbaji a karamar hukumar Rogo sun cinnawa gidaje 10 wuta.

Kamar yadda Vanguard ta rahoto, sakataren hukumar bada agajin gaggawa na Kano, Saleh Jili, ya ce hukumar ta mika sakon jaje ga wadanda abin ya shafa kuma ya ce sun kai musu kayan tallafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel