Mazauna Kauye Sun Gudu Yayin Da ’Yan Ta’adda Suka Kashe Mutane 19 a Zamfara
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, 'yan ta'adda sun hallaka mutane 19 a wani yankin jihar Zamfara, Arewa maso Yamma
- 'Yan ta'addan sun kuma jikkata mutane da dama, wasu mazauna kauye sun tsere zuwa wasu kauyukan da ke kusa
- Hakazalika, sun sace kayayyaki masu daraja na mazauna kauyen, ciki har da kayan abinci da dabobbi masu hyawa
Zurmi, jihar Zamfara - ‘Yan ta’adda sun hallaka mutane 19 a wani mummunan harin da suka kauyen Riyoji a gundumar Birnin Tsaba, karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Punch ta ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun kuma jikkata mutane da dama a harin da suka kai da misalign karfe 10 na daren ranar Laraba.
Wani mazaunin yankin, Muhammad Lawan ya shaidawa jaridar ta wayan tarho cewa, ‘yan ta’addan sun farmaki kauyen ne a kan babura, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
A kalamansa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Kwatsam da suka dura kauyen, sai suka fara harbin duk wanda suka hadu dashi, sun kashe mutum 19 kuma sun raunata wasu. Mutane da yawa sun kubuta saboda sun gudu cikin daji don tsira da rayukansu."
‘Yan bindiga sun sace kayan abinci da dabbobi
Ya kuma bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun kutsa, inda suka sace kayayyaki masu daraja da suka hada da abinci da dabbobi.
Ya kara da cewa, mazauna kauyen, musamman mata da yara sun tsere zuwa kauyukan da ke kusa don tsira da rayukansu, Platinum Post ta tattaro.
Lawal ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki ta hanyar kawo jami’an tsaro yankin domin kare su daga yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda.
An yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, amma hakan ya ci tura.
Hakazalika, kwamishinan yada labaran jihar, Ibrahim Dosara bai dauki waya ba sadda aka kira shi, bai kuma dawo da sakon tes da aka tura masa ba.
An janye batun ci gaba da tsare Tukur Mamu
A wani labarin kuma, hukumar SSS ta ce ta janye batun da ta shigar na ci gaba da tsare Alhaji Tukur Mamu mai tattauna da 'yan bindiga a jihar Kaduna.
A tun farko an kama Mamu ne bisa zargin hannu a ayyukan ta'addancin da ke faruwa a Arewacin Najeriya.
An kama shi ne a kasar Masar yayin da yake shirin shigewa kasar Saudiyya domin yin aikin Umrah a can.
Asali: Legit.ng