Gwamnatin tarayya Za tayi Karin Albashi, An Bayyana Ma’aikatan da Abin Zai Shafa
- Gwamnatin tarayya ta yarda akwai bukatar a duba tsarin albashin CONMESS da CONHESS a Kasar nan
- Ministan kwadago da samar da ayyuk, ya goyo bayan likitoci da suka kawo masa kukan rashin karin albashi
- Dr. Chris Ngige ya nuna tun farko ya kamata a ce gwamnati ta kara masu albashi saboda asibitoci su rika aiki
Abuja - Gwamnatin tarayya ta sha alwashin yin rigakafi domin ganin likitoci da sauran malaman lafiya sun daina zuwa yajin-aiki a asibitoci.
The Nation ta fitar da rahoto a ranar Juma’a, 25 ga watan Nuwamba 2022, wanda ya nuna za a kawo gyara a tsarin albashin CONMESS da CONHESS.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Dr. Chris Ngige ya kyankyasa wannan a lokacin da ya zauna da ‘yan kungiyar NMA da NAMDA.
Ngige ya yi zama da Shugaban kungiyar Likitoci da sakatarensa; Uche Ojinmah, Jude Onyekwere da irinsu shugaban kungiyar NAMDA, Nosa Orhue.
Kukan da NMA take yi
A wajen wannan zantawa da aka yi, shugaban kungiyar NMA ya jero kalubalen da likitoci suke fuskant a Najeriya, a nan ya kawo batun CONMESS.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A matsayinsa na Mataimakin darektan hulda da jama’a da manema labarai na ma’aikatar kwadago, Olajide Osundun ya fitar da jawabi bayan taron.
Jawabin Osundun ya nuna kungiyar NMA ta ankarar da Ministan cewa tun a 2009, an yi alkawarin za a rika duba albashinsu duk bayan shekaru biyar.
Shekaru fiye da goma da yin wannan magana, gwamnatin tarayya ba ta karawa likitoci albashi ba.
Daga ma'aikatar lafiya zuwa ma'aikatar kwadago
Rahoton ya bayyana cewa Dr. Uche Ojinmah ya koka a kan yadda ma’aikatar lafiya ta gagara shawo kan sabanin da ke tsakanin ta da Likitoci.
Ganin yadda abubuwa ke tafiya, Dr. Ojinmah ya bukaci Ngige ya shiga tsakaninsu, ya tabbatar da an cika masu alkawarin nan kafin 11 ga Disamba.
Ngige ya goyi bayan Likitocin, yace shi ma a ra’ayinsa akwai bukatar a duba tsarin albashin CONMESS da CONHESS tun kafin a kai ga yin rigima.
Amma Ministan ya bayyana cewa idan har maganar ta koma ofishinsa, likitoci ba su da damar tafiya yajin-aiki kamar yadda dokar kasa tayi tanadi.
Tittin Buhari a Niamey
Muhammadu Buhari ya tafi kasar Nijar domin halartar taron kungiyar AU, sai ga shi labari ya zo cewa ya kaddamar da wani titi da aka gina a Niamey.
Abin sha’awar, Garba Shehu yace an sa wa titin sunan Shugaban Najeriya ne a dalilin irin kauna da girmamawar da ake yi masa a kasar makwabtan.
Asali: Legit.ng