Hukumar NDLEA Ta Kama Tan 1.5 Na Miyagun Kwayoyi a Jihar Katsina

Hukumar NDLEA Ta Kama Tan 1.5 Na Miyagun Kwayoyi a Jihar Katsina

  • Hukumar NDLEA ta yi nasarar kame wasu mutane da ke ta'ammuli da miyagun kwayoyi yankuna daban-daban na jihar Katsina
  • An kuma kama tarin kayayyakin bugarwa a jihar, hukumar ta bayyana adadin kayayyakin da aka kwato
  • Hukumar NDLEA ta sha bayyana irin kayayyakin da suka kama a hannun jama'a masu nasaba da miyagun kwayoyi

Jihar Katsina - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kame tan 1.5 na miyagun kwayoyi tare da kama wadanda ake zargi 993 a jihar Katsina daga ranar 10 zuwa 23 ga watan Nuwamba.

Kwamandan NDLEA a jihar, Muhammad Bashir ne ya bayyana hakan ga manema labarai kan ayyukan hukumar a iya lokacin da ya bayyana, Punch ta ruwaito.

Da yake jawabi, ya bayyana lokacin da ya karbi ragamar tafiyar hukumar a jihar a matsayinsa na kwamanda na 16 da aka tura jihar.

Ya kuma bayyana irin ayyukan da ya jagoranta da suka hada kama kaya, ‘yan ta’adda da sauran ayyukan da suka shafi harkallar miyagun kwayoyi a fadin jihar da tsallake.

NDLEA ta kama kayayyakin kwaya a jihar Katsina
Hukumar NDLEA Ta Kama Tan 1.5 Na Miyagun Kwayoyi a Jihar Katsina | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“Kokarinmu ya kai ga sakamako mai kyau na kama mutane 993. Sun hada da maza 977 da mata 16.
“Jumillar miyagun kwayoyi da aka kama a cikin lokacin su ne kilogiram 1,555,446. Wannan ya hada da kilogiram na 1,473,795 na tabar wiwi, kilogiram 81,651,39 na kayan bugarwa da maganin muran kodin da ya kai lita 92.95."

Wadanne irin mutane ne aka kama?

Kwamandan ya kuma bayyana cewa, akasarin wadanda aka kaman basu wuce shekaru 16 zuwa 40 ba, People Gazette a ruwaito.

Bashir ya kuma bayyana cewa, wani sashe na hukumar ya yi nasarar gyara halin mutum 76 daga kawo shi.

A cewarsa:

“Hudu daga cikin mutanen suna da cutar jarabar shan kwaya kuma ‘yan asalin kasar Nijar ne."

Daga karshe ya yabawa gwamna Masari da irin kokarin da yake da kuma tallafawa hukumar da yake a kowane lokaci.

A wani labari mai kama da wannan, hukumar NDLEA ta kama wata mata mai shekaru 56 da kayayyakin da ake zargin miyagun kwayoyi ne.

An kama ta ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel