Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin dauri kan dan tsohon shugaban fansho Maina bisa laifin almundahana
- Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kotun tarayya ta yankewa dan Abdulrasheed Maina, faisal
- Hakazalika, ta zaftare wasu shekaru daga hukuncin da aka yankewa Faisal a baya, tare da bayyana dalili
- An tsare dan tsohon shugaban hukumar fanshon ne tare da mahaifinsa bisa laifin hada baki da sace kudaden kasa
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara mai zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin daure Faisal, dan tsohon shugaban hukumar fansho da aka rusa, Abdulrasheed Maina bisa laifin hada baki da sace kudin kasa, The Nation ta ruwaito.
A hukuncin da kotun ta yanke a yau Alhamis 24 ga watan Nuwamba, alkalai uku da suka yi zama sun rage wa'adin da aka diba masa na shekaru 14 zuwa bakwai tun da wannan laifinsa ne na farko.
Mai shari'a Ugochukwu Anthony Ogakwu da ya jagoranci hukuncin ya bhayyana bayyana cewa, mai shari'a Okon Abang n kotun tarayya da ke Abuja ya yi gaskiya wajen daure Faisal.
Sai dai, inda ya saba da kotun daukaka kara, bai yi la'akari da wannan ne laifin Faisal na farko ba, don haka kotun ta rage masa wa'adin da aka diba masa, rahoton Vanguard.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Laifukan da suka ja aka daure Faisal Maina
EFCC ta gurfanar da Faisal Mana ne bisa aikata laifuka guda uku da suka shafi almundahana da sace kudin kasa, inji rahoton jaridar TheCable.
A ruwaito cewa, Faisal na amfani da wani asusun bogi na bankin UBA, wanda mahaifinsa ya yi amfani dashi wajen zuba kudaden da suka kai N58.1m, kuma ana zargin mahaifin nasa ya saci kudin ne.
Hakazalika, an gano cewa, an sanya kudi a asusun mai suna Alhaji Faisal Farm, wanda shi Faisal da mahaifinsa suka cire daga baya a Oktoban 2013 da Yunin 2019
Duba da wadannan laifukan ne aka daure shi shekaru 14 a gidan yari a 2021.
An gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna
A wani labarin kuma, an sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Muktar Yero bisa zargin aikata almundahana.
A baya EFCC ta gurfanar dashi a kotu, amma aka ba da belinsa kana maganar ta yi shuru na wani dan lokaci.
A wannan karon ma an ba da belinsa kana kotu ta dage karar zuwa badi.
Asali: Legit.ng