Matashiyar ’Yar Gwagwarmaya da Ke Fafutukar Maza Su Rinka Kara Aure a Cikin Al’umma

Matashiyar ’Yar Gwagwarmaya da Ke Fafutukar Maza Su Rinka Kara Aure a Cikin Al’umma

  • Wata matashiya 'yar Najeriya ta zo da sabon batun da ba a saba gani ba, inda tace tana son maza suke kara aure
  • Zainab Umar, wacce 'yar asalin jihar Adamawa ce ta bayyana hakan ne a wata hira da aka da ita a kafar labarai ta BBC Hausa
  • Ta kuma bayyana irin mijin da take so ta aura a nan gaba tare da bayyana kadan daga tarihin gidansu

Najeriya - Wata matashiya 'yar asalin jihar Adamawa mai shekaru 25, Zainab Umar ta zo da sabon salo yayin da ta bayyana fafutukar da ta dauko na wayar da kan mata su rungumi kishiya hannu biyu.

Zainab ta bayyana ra'ayinta, inda yace ta fahimci mata sun fi maza yawa, don haka akwai bukatar kowane namiji ya kara aure saboda kiyaye faruwar barna a waje.

Kara karanta wannan

Mun tuba: PDP ta tafka kura-kurai daga 1999 zuwa 2015, Atiku zai gyara komai

Ta kuma ba da kadan daga tarihin gidan da ta taso, inda tace mahaifiyarta ba ta da kishiya, amma ita dai ba za ta iya rayuwa babu abokiyar zama ba.

Budurwa mai fafutukar ganin maza sun kara aure
Matashiyar ’Yar Gwagwarmaya da Ke Fafutukar Maza Su Rinka Kara Aure a Cikin Al’umma | Hoto: bbc.com/unsplash.com
Asali: UGC

Ta shaidawa BBC Hausa cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Duk da cewa mamata ita kadai ce a gidanmu, amma wannan ba zai hana ni fafutukar da nake ba."

Maza a kara aure, mata a yi hakuri a fahimta, inji Zainab

Matashiyar ta kuma yi tsokaci da cewa, ya kamata maza su kara harama, su dauki niyyar karin aure bisa gaskiya da amana tare da mutunta ta ciki da wacce za a auro.

A ra'ayin Zainab, tuni mata suka fara sauke farashi, kowacce so take a yi wuf da ita saboda yadda lamurra suka yi tsami a cikin al'umma.

A bangare guda, ta ce ita a yanzu bata da aure, kuma ba za ta iya auren wanda bai da mata ba.

Kara karanta wannan

Shin Najeriya kasar addini ce? Jigon siyasan Arewa ya bayyana matsayin Najeriya game da addini

A kalamanta:

"Idan na samu mai mata uku zan aura, inda na samu mai mata biyu zan aura, amma dai kaddara ce za ta sa na auri wanda bai taba aure ba. Bana son na rayu bani da kishiya saboda ni ban ga aibunta ba."

Sanannen lamari ne a duniya yadda mata ke kai makurar kaucewa hanya don ganin sun rayu babu kishiya.

A wani labarin na daban, tuni maza a Adamawa suka gano hanyar za ga uwar gida tare da yin sabuwar amarya ba tare da saninta ba.

Wata kalma 'Permanent Day' da maza ke amfani da ita wajen yin aure ba tare da hauragiya da fushin uwar gida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.